Sarkin Karshi ya karbi bakuncin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kyau yayin da ya ziyarci fadarsa Kamar yadda ya saba, idan ya je kamfe a gari, ‘Dan takaran NNPP ya kan ziyarci Sarakuna da ke mulki Muhammad Sani Bako III ya ba Kwankwaso sarautar Jarumin Karshi da ya je mika gaisuwa a ranar Litinin 

A ranar Litinin, 16 ga watan Junairu 2023, Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa suka ziyarci Sarkin Karshi watau Alhaji (Dr) Muhammad Sani Bako III. ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan tawagarsa sun je yawon yakin zabe ne a jihar Nasarawa. 

A farkon makon nan jam’iyyar NNPP ta gudanar da babban taron yakin neman zabenta na jihohin Arewa maso tsakiya, an shirya taron ne a birnin Lafia. 
Previous Post Next Post