Mata da yawa na ganin ƙirjin mace kimar ɗiya mace ne kuma abin tinƙaho ne ga mace da jan hankali ga maza da kuma birgewa. Don haka mata da yawa sun ɗauki gyaran mama wani muhimmin abu, musamman bayan shayarwa ko faɗuwar nonuwan budurwa a gida ko rashin girman sa.
Girman mama an alaƙanta shi daga cikin abubuwa wanda ke sa mace a ganta mai kyakkyawar halitta da ban sha’awa da birgewa ga maza kasancewar maza mafi yawa na son mata masu wannan yanayi. Wannan lamari nada tasiri sosai ga tunanin mata da yawa, ta yanda wasu ke jin alfaharinsu da tinƙaho zai faɗi idan maman su ya faɗi ko suka bari ya canza daga sigar da ake bege. Shi dai nono wani dandazo ko cincirundon tsokar nama ne mai zagaye da kitse daya taso sama a ƙirjin mace baliga. Tsokokin suna canzawa lokacin balaga, haila, juna-biyu da lokacin shayarwa, da kuma lokacin barin al’adar mace (menopause). Waɗannan tsokoki kuma zasu iya buɗewa su ƙara girma saboda wasu magunguna ko tsirran magani.
Mata da yawa ne ke neman magani a kasuwanni domin gyaran mama kuma hanyoyin gyaran maman da ake bi suna da yawa amma amma a zahiri ingancinsu kaɗan ne, wanda sun hada da: ƙwayoyin magani, man shafawa, famfon iska na ƙara girman mama (breast pump), gari , ofireshin/tiyata (surgery)domin ƙara girman nono da sauransu . Wasu hanyoyin nada hadari ga lafiya, kuma sakamakon amfani da magungunan ko hanyoyin ya sha banban tsakanin mata masu ta’ammuli da magungunan, inda wasu sun sami nasarar ƙara girman mamansu wasu kuma babu wani canji.
1. HULBA (Fenugreek) da man ta (oil).
2. SHAMMAR (Fennel seeds)
YANDA ZA’AI AMFANI DASU
A sami ƴaƴan hulba da ƴaƴan shammar a Islamic Chemist sai a niƙe su , a dake su sosai amma kowanne daban-daban. Haka kuma za’a iya samun garin nasu a Islamic Chemist ba sai an sha wahalar daka ba. Sai a ɗibi cikin ƙaramin cokalin shayi na garin hulbar guda (1 teaspoon) a zuba a kofi , sa’annan a ɗibi garin shammar ɗin shima cikin ƙaramin cokali guda a haɗe su a kofi ɗaya ( hulba + shammar). Sai a tafasa ruwan zafi idan ya tafasa sai zuba cikin kofin maganin a motsa da cokali sosai a sa’annan a rufe bakin kofin. Idan yayi minti 10 arufe – ya jiƙa sai a tace da rariya a zuba zuma ga ruwan da aka tace asha. Sa’annan a shafa man hulba ga mama safe da dare. Ashafa man a linda/luliya (massage) ya shiga fatar nono sosai. Za’a yi hakan (yin shayi da shafa man hulba) sau biyu (2) a rana – safe da dare har na tsawon wata daya. Za’a ga cikakken sakamako bayan wannan lokaci da yardar Allah. Daga zuwa wannan lokaci ko kafin lokacin mace zata fara jin nonuwanta sun kara nauyi, wanda alamace na girma da suke karawa. Kara girman nono ba abu bane dake faruwa cikin dare daya kamar yanda wasu ke tunani. Don haka akwai bukatar hakuri kamin aga sakamakon da ake bukata.
Man hulba yana da amfani idan aka jure ana amfani dashi. Yana da amfani 2: Na farko, yana sanya gudanar jini da kyau wajen nono wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar nono da kyawon fatar nono. Na biyu, yana buɗe tsokokin nono yanda zasu ƙara girma da ƙarfin fata (firming) mai riƙe nono tsaye ba mai yawan taushi ba wanda kesa mai sanya mama ya sunkuya saboda yawan taushi. A nemi man hulba ɗan Misra ko Hemani (Pakistani). Allah Ya taimaka.