Wani matashi mai suna Halifa Hamza mazaunin unguwar Kurna a birnin Kano, ya cakawa wansa mai suna Usman Hamza Almakashi a ƙahon zuciya wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

 

Rahotannin sun ce al’amarin ya faru ne lokacin da marigayin ya yi wa ƙanin nasa magana domin ya cire masa wandonsa.

 

Daganan ne sai wanda ake zargin Halifa ya fusata har ya shiga gida ya ɗauko Almakashi ya cakawa wan nasa a ƙirji wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

 

Tun farko mahaifin su mai suna Alhaji Hamza, ya musanta labarin da ke cewa sun yi faɗa ne akan wata Mage.

"Marigayin ya yi masa magana ne akan wandonsa da ya gani a jikin sa , bayan ya ce, ya cire , shi ne kanin ya fusata, har wannan lamari ya faru.

 

Rahotanni na cewa wanda ake zargin da hallaka ɗan uwan nasa ya cika wandon sa da iska.

 

Har ya zuwa wannan lokaci da muke haɗa wannan labari,  rundunar ‘yan sandan jihar Kano bata ce komai ba kan faruwar lamarin.

Previous Post Next Post