Yaudarar maza yanzu tafi yawa “wasu” sau tari namiji ya sani ba aure zaiyi ba haka nan bashi da niyyar yin aure amma sabod san zuciya sai yayi ta yaudar/lalata ya’yan mutane wasu ma daga cikin mazan har alfahari suke yi sbd yawan yan matan da suka lalata, kuma abun takaici kowacce idan suka je mata to suna zuwa da zancen aure amma da hakar su ta cimma ruwa to zaa neme su a rasa!!!
Sun gudu sai kuma suje wajan wasu Yan matan,irin wadannan samarin shahon sun kware wajan iya daukar hankalin mace da mayaudaran kalaman su wanda iyakar bakin sune yake tsayawa.
Sun kware wajan saka mace ta mace akan kaunar su,sai sunci galba a kan ta,daganan kuma sai a neme su a rasa sun gudu.
irin wannan lokacin ne za’a ga budurwa tana kuka sosai idan aka tsaurara bincike bawai iya kukan gudunwar tasa take ba aa akwai wani boyayyen Al’amari daya faru tsakanin su, shiyasa duk wadda aka yaudara indai har tasan bata bada kanta ba to Alhmdulillah komai yazo da sauki tayi wa Allah godiya shi kuma yaje can ya karata da yaudaran sa domin sai Allah ya Miki sakayya.
★Ana yawan fadawa maza wannan kalmar #KOMAI NAMIJI YAYI ADONE??? wannan kalmar tama da ina rudar masu wannan halin sbd sam ba abin ado bane,sbd idan ka lalata yar wasu zai zame maka mugun Ado daga lokacin da’aka fara lalata naka ya’yan ko kuma wataran aka wayi gari matar ka tana cin Amanar ka, duk wadannan abubuwan basu da dadi,, idan kace bazaa gani Ajikin kaba to ai baa yiwa Allah wayo dolen kane ka gani Ajikin zuri’arka idan ma baka gani ba zaa ganema, shidama wannan ai bashine ko baka biya ba zaa biyama babu ko sisi.
★SAURAYIN RAGE DARE, wasu da yawa irin wannan sunan ake fada musu sbd abin nasu ya wuce lissafi yau suna wajen waccan gobe waccan!,,,,,,,
Basu da tsayayyar budurwa daya,zasu tsara mace fiye da tunanin ta yadda zata na zaton ita kadai ce a cikin zuciyar sa,irin wadannan samarin wasu har kudin aure suke kawo wa,amma idan bukatar su ta biya su tafi daman abinda sukayi niyya kenan.
Wani ma idan suka tashi yaudarar sai suce an musu mata A gida Alhali karyane kawai hakarsu tagama cimma ruwane sun samu Abinda suke so,wani kuma ma bazai gaya miki ba sai dai ki neme sa ki rasa,Yan mata ku kula wajan rike mutuncin ku fa.
#ya kama ta masu wannan hali su ankare sbd a wannan zamanin da muke ciki tun kana dunia Allah yake fara nunama iyakacinka/sakayya,,,, idan kayiwa budurwar ka wayo ka raba ta da mutuncin ta karkayi murna sbd baka isa kakare naka daga masu irn halinka ba A lokacin da zaa lalata su bakama wajen a sannan zaka ji irin radadin da iyaye suka je lokacin da suka san an lalalata masu yara.
sannan idan ka guji wadda ka lalata baka isa ka guji wadda wani ya lalata ba karshe kaje ka auri bugun wani kato
Alamomin munafiki guda uku ne duk wani saurayin shaho sai ya taka su duka
Karya
Rashin cika Alkawari
Ha’inci
yanzu fisabilillahi inna amfanin hakan gaba daya ya kamata masu wannan dabi’a suyi wa kan su karatun ta nutsu kodan goben su tayi kyauuu,a dinga tunawa mutuwa bata sanarwa mutum lokaci.
masu wannan hali Allah yashirya ku Ameen
Mushakata Da Wannan
Hanyoyin rabuwa da budurwa batare da tayi tunanin yaudararta kayi ba…
1. 16 missed calls?… Kin kashe mini Battery, nan gaba idan banyi wasa ba ni zaki kashe. Don haka ta ƙare ni dake. Tayaya zanzo zance sauro ya dinga cizona ke bazai cijeki ba?Bazaki sake ganina a ƙofar gidanku ba.. Bakya girmama ni ina magana amma ke numfashinki kawai kikeyi ko?n gama.
4. Na kira ki kin wani ɗauka da wurwuri, bakida haƙuri kwata kwata. Ni kuma bazan ya auren mara hakuri ba, don haka sai watarana.
5. Meyasa kike share inda zan zauna da tsintsiya alhalin kinsan ni ɗan PDP ne? Bakya girmama ra’ayina don haka Ni kinga tafiya ta sai watarana
6. Koda yaushe idan namiki message saidai kiyimin reply da abbreviation, wato kinaso mu haifi yara guntaye ko?
7. Nace miki ina son abinci me zafi shine kika kawo mini ice cream me sanyi, baki damu dani ba don haka ba maganar aure.
Na tafi
8. Baby na ya kake? Ke don bakida albarka ni ne baby? Ki rasa wanda zaki kira baby sai ni? Toh kije ki nemi wani saurayin ba dai ni ba mun rabu.
9. Ke nifa da kike gani in kin aure ni ko waya bazaki rike ba, don haka ki kyautar da wayanki ko kuma mu rabu da juna oh ni kike harara ta waya ko toh mun rabu Fateemah Ali