Muhimmancin Yarda Da Juna A Tsakanin Ma’aurata:
Ma’aurata:☈
Yarda na nufin amincewa da bambamcin halayya da ke tsakanin juna. A cikin zamantakewa na aure, yarda da juna yana nufin sadaukarwa ga abokin zama tare da girmama juna a zahirance da sauraron juna lokacin da ake bukatar tattaunawa. Ba a bukatar boye wa abokin zama abubuwan da suke damun juna a cikin auratayya.
Dole ne a samu girmama juna a cikin zamantakewar aure idan ana so a yi zama mai daurewa tare da karfafa wa juna kwarin gwiwa. A cikin zamantakewar aure bai zama dole sai an bayyana wa juna duk abin da ya shigo cikin zuciya. Zai iya kasancewa ana da wani abu na kashin kai wanda z aka boye a cikin zuciyarka ba sai ka fada wa abokin zama ba.
Yarda da juna ba wai yana nufin dole sai an yi musayan kayayyaki da juna, kamar irin su wayar salula da kwafuta da dai sauran su. Za a iya musayar wadannan kayayyaki a lokacin da aka samu lamari na gaggawa. Amma idan ba haka ba, ba a bukatar duba wa juna wadannan abubuwa domin suna haddasa rikici a cikin zamantakewa.
Idan aka samu rashin jituwa a tsakani, akwai bukatar a dawo da aminci a cikin zamantakewa. A nan ga wasu hanyoyi da ya kamata a bi wata kila za su iya aiki cikin gaggawa ko kuma nan gaba kadan.
A yi kokarin duba dalilan da ya sa aka samu wannan matsala kar a damu da girman bacin ran da aka samu, domin abokin zama na iya yin wasu abubuwa saboda bacin rai. Zai iya yuwa an samu bacin ran ne sakamakon rashin mahimta ko rashin yin bayani. Duk abin da ya janyo ma, yana da matukar mahimmanci a san dalilan da ya haddasa wannan matsalar, sanin hakan zai taimaka wajen bayar da damar sake gina zamantakewar mai daurewa a nan gaba. Haka kuama idan an samu rashin jituwa a tsakani, a bai wa juna damar yin bayani cikin natsuwa tare da bai wa juna hakuri da wanda ya yi laifi da kuma wanda bai yi ba. Domin shi bayar da hakuri yana da matukar mahimmanci a cikin zamantakewar aure lokacin da aka samu sabani. Sannan a daina dawo da abin da ya wuce lokacin da aka sami sabani, domin dawo da abubuwan da suka wuce suna kara ruruta sabon hayaniya.