Wata matashiyar sojan ruwa ƴar Najeriya ta koka kan rashin samun mashinshini da take fama da shi Kyakkyawar budurwar ta bayyana dalilin da ya sanya samari da dama ba su iya tunkarar ta da batun soyayya Bidiyon matashiyar ya ɗauki hankula sosai inda mutane da dama suka yi ta sharhi akan sa.
Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya, mai amfani da sunan @naval_goddess a TikTok, wacce ke aiki da rundunar sojojin ruwan Najeriya, tayi wani bidiyo da ya ɗauki hankulan mutane. Matashiyar budurwar ta ɗora wani ɗan gajeran bidiyo a TikTok inda ta nuna yadda samari ke tsoron ta saboda khakin ta na soja.
Ta bayyana cewa duk da tana da matuƙar son ganin ta samu saurayi, hakan yayi mata wahala saboda yanayin aikin ta. Nan da nan samari da dama suka yi ta yin tururuwa a ƙasan wajen yin sharhi kan bidiyon, suna ƙoƙarin jaraba sa'ar su.
Bidiyon ya yaɗu sosai Bidiyon ya yaɗu sosai inda sama da mutum dubu shida suka yi sharhi akan sa, sannan sama da mutum dubu arba'in da takwas suka danna masa alamar so. Ga kaɗan daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Legit Hausa ta tattaro: