Jarumar Ta gamu da tsautsayin da ya fada mataa masana’antar har ya jawo mata kora. tarihi dai ya nuna itace jarumar film ta farko da aka Taba korarta a masandantar.
A wata hira da tayi da kafar yada labarai ta THE GUARDIAN, tauraruwa Rahama ta bayyana cewa an so tafito a wani fim din ta na kudu a matsayin yar
madigo wato lesbian, amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta
fito Wato arewachin Nigeria.
da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damanmaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin Duniya.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin
bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da
hakan.
Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba
dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana
Sand ar ta.
Ga Bidiyon Sai Ku Kalla Kuji Cikakken Bayani:
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Game Da Abunda Rahama Sadau Tace, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.