Wasu 'yan daba a ranar Asabar sun farmaki tawagar matar Gwamna Ahmadu Fintiri, Lami Ahmadu Fintiri a jihar Adamawa Sun tare tawagarta a garin Muchala da ke yankin Mubu inda suka yi musu ruwan duwats da sandu kafin su sha da kyar Duk da matar gwamnan bata smau rauni ba, daya daga cikin 'yan tawagarta ya samu rauni a kai amma yana samun sauki
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin a takardar da ya saki ga manema labarai a Yola ranar Lahadi.
Yace an kai farmaki kan tawagar motocinta ne a garin Muchala da ke yankin Mubi inda wasy bata-gari suka dinga jifansu yayin da suka shiga wani kauye halartar taron matan Katolika. 'Yan daban da ke dauke da duwatsu da sanduna sun ragargaza mota kirar bas mai mazaunin mutum 18 da ke dauke da manema labarai kuma sun rauna wani mutum daya mai suna Dauda, Daily Trust ta rahoto. Daya daga cikin wadanda ke cikin tawagar da baya so a kira sunansa saboda bashi da damar tattaunawa kan batun, ya sanar da Daily Trust cewa matar Fintiri bata samu rauni ba kuma bayan nan ta koma Yola yayin da Dauda da ya samu a rauni a kai yake samun sauki. Takardar da 'yan sandan suka fitar ta ja kunnen masu tada fitina kan cewa ba za su ci banza ba saboda rundunar ta shirya tabbatar da zaman lafiya a jihar inda ta kara da cewa an aike jami'ai don cafko maharan.