Bishiyar jir jir anayi mata lakabi da bishiyar waraka, saboda ‘ya’yanta da ganyenta da man dake jikinta duk ana sarrafasu wajen magance cututtuka ajikin Dan Adam. Man jir jir yana daga cikin nau’in magungunan da aka dade ana amfani dasu saboda muhimmancinsu da kuma amfaninsu.

Man jir jir yana da tarin aikin da yake a jikin dan adam kamar yadda zamu zaiyano muku kamar haka;

– Man Jirjir yana Qara Qarfin Jima’i ga Maza. Kamar mutumin da yake da Qarancin sha’awa, ko kuma rashin Qarfi, idan yana Shan Man Jirjir acikin ruwan dumi ko kuma shayi ba madara.

– Wanda yake da Qarancin Jini ajikinsa, idan yana shan Man jirjir ko kuma Garinsa, zai samu Qaruwar jinin jikinsa. Haka kuma masa fama da ciwon daji, bincike ya nuna cewar Jirjir yana kashe 97% na Kwayoyin cutar daji, musamman masu sankaran mama wato ciwon nono.

– Matar da Jinin al’adarta ya rikice, sai ta samu Man Jirjir ta dinga zuba cokali daya a ruwan dumi tana sha, zata samu waraka da yardar Allahu. Sai dai amma kuma fa Matar da take dauke da Juna biyu kada tasha Man Jirjir domin kuwa yana matso Wuyan mahaifarta kuma zai iya haddasa mata ‘bari ko nakuda cikin gaggawa. Don haka akiyaye

Abinda za’a nema sune ko nace shines;

– Man jir jir
– Garin jir jir
– Ganyen jir jir

Duk wanda akayi amfani dashi ya wadatar. Cinsa ko shansa kawai ya wadatar shi Man jir jir yana kone majinar kwankwaso, da majinar ƙirji. Don haka yana ƙarawa namiji ƙarfin mazatuka.

Allah yasa mudace.


Previous Post Next Post