Saboda haka yana da kyau da kuma fa’ida sosai a wurin ki ki daure ki dinga yawan sha da kuma sarrafa su ta hanyoyi mabambanta domin jindadi da kuma yalwar lafiya a tattare da ke.
Ga kadan daga jerin abubuwan da zaki nema domin yin hadin:
Madara
Kankana
Madara
Abarba da Ayaba
Gwanda
Lemo
Sukari
YADDA ZAKIYI WANNAN HADI:
Domin sanin kowanne makamar aiki, dole sai an koyawa mutum ko kuma an bashi darasi, to don haka muma ga yadda za’a hada kayayyakin nan idan ana son samun biyan bukata kamar yadda ake so.
Yar’uwa ki sami kankana ki yankata sai ki sami bulanda mai kyau ki murjeta kamar an markada, itama abarbar kiyi mata haka, ki cire bakin idonta, gwandar ki markade ayar kuma ki dameta kamar fura, lemon kuma kiyi masa sala-sala, sannan a sa a bulanda matse shi.
Bayan kin gama matse su, sai ki tace su ki saka sukari, da madara, sai ki dama, sai ki sa a firji ko ki daure a Leda ki sami kankara ki Dora a Kai idan Yayi sanyi sai ana sha.
Haka zalika wannan hadin yana sanya mata su jisu cikin ni’ima a koda yaushe.
Idan dai anyi kamar yadda aka ambata, to lallai za’a ga abin mamaki akan cikowar wadannan sassan jiki.
Allah yasa mudace.