Allah sarki: Magidanci me Shekara 80 da Yara 20 da Mata 4 yace yau kwana 5 ba'a Dora Abinci ba a gidansa sakamakon banki sun hanashi kudi cash.

Magidancin ya shaidawa gidan jaridar Rariya cewa yau kwana 4 kenan ba'aga hayaki ba a gidansa sakamakon banki sun hanashi kudi Kuma ATM dinsa baya aiki saidai ya amsa a cikin banki.

Yace kullum da asuba yake futowa ya tafi banki tsawon kwana Biyar dinnan Amma abin haushi sai layi yakusa zuwa kansa sai ace kudi sun Kare ko Kuma ba network.

Haka yaci gaba da cewa gashi Yana da kananan Yara wadanda basusan babu ba inda yake bada Labarin a cikin kuka.

Allah ya kyauta.
Previous Post Next Post