Kotun masana'atu ta soke dokar da rundunar 'yan sandan Najeriya ta saka na kange jami'anta mata daga yin ciki ba tare da aure ba, TheCable ta ruwaito. A ka'idar da rundunar ta kawo na aiki a sakin layi na 127, duk wata jami'ar da ta dauki ciki ba tare da aure ba za a kore ta a aiki.
A baya kunji wani rahoton da yake cewa, wata mata a rundunar 'yan sandan Najeriya, Omolola Olajide ta yi, wannan yasa aka kore ta a aiki a shekarar 2021.
Kwamishinan 'yan sanda, Babatunde Mobaya ya ce an kori wannan jami'ar ne daidai a tanadin dokar 'yan sanda sashe na 127.