Alkalin alkalan jihar Oyo, Mai shari'a Munta Abimbola, ya saki wata dattijuwa yar shekara 65 da jikanta dan shekara 15 da ake tsare da su kan zargin satan kaji guda biyu Mai shari'a Abimbola ya ce an saki kakan da jikanta ne sakamakon afuwa da aka musu saboda yawan shekarunta da rashin lafiya sannan jikanta yaro ne wanda bai balaga ba Ma'aikatar shari'ar ta jihar Oyo karkashin jagorancin alkalin alkalan sunyi wannan afuwar ne ga mutanen da ake tsare da su kuma gabanin shari'a amma suna da kallubalen rashin lafiya, yawan shekaru da tsawon zama a gidan yarin.

Dattijuwar da jikanta suna tsare a gidan gyaran halin tun watan Disamban 2022 suna jiran shari'a. An yi zargin cewa yaron ya sace kaji biyu ya kuma bawa kakansa don ta ajiye masa. Mai shari'a Abimbola ya ce sun cancanci afuwa saboda yaron bai balaga ba kuma dattijuwar ta tsufa gashi bata da cikakken lafiya. Ya gargade su kada su sake su koma yin sata ko kuma karbar kayan sata, The Eagle Online ta rahoto. 


Previous Post Next Post