
Dan uwa idan kana so a duk lokacin Saduwa da iyalin ka ka gamsar da ita har ta kawo ruwa to ga hanyar da za kabi.
Wannan magani da zamu baku yana aiki sosai indai akan matsalar saurin kawowa ne ko rashin jima’i fiye da sau ɗaya.
Amma sai dai wannan magani idan kana da matsala ta karancin maniy ko tsinkewar maniyyi kar kayi amfani da shi.
Sannan karka sake kayi amfani dashi wannan maganin har ya wuce kwana uku Amma insha Allah daga ranar daka fara amfani dashi zaka ga sauyi sosai,kwarai da gaske.
ABINDA ZA’A NEMA DOMIN HAƊA WANNAN MAGANIN:-.
-Madara ta Ruwa
-Garin Kimba (Negro pepper)
YADDA ZA’A HAƊA SU SHINE:-.
Da farko za’a samu madara ta ruwa rabin ƙaramin gwangwani za’a zuba a kofi,sannan za’a zuba garin Kimba rabin karamin chokali za’a jujjuya sosai sannan sai asha,ana shane minti 30 kafin a kusanci iyali.
Insha Allah Za’ayi mamaki.
Allah yasa mu dace.
ABIN DA YA KAMATA KUSANI DANGANE DA DAREN FARKO GA MA’AURATA
SAMARIN MU DA YAN MATAN WANNAN ZAMANI SAI MU GYARA GASKIYA
Idan ango ya shigo dakin sabuwar amaryar sa, bayan ya zauna, sai ya yi mata sallama cikakkiya, watau: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu,’
Ita ma sai ta amsa da irin haka, watau: ‘wa’alaikumus salamu wa rahmatullahi wabarakatuhu.’
Hakan Ya fi kyau ya haɗa da miƙa mata hannu su yi musabaha tare da sallamar.
Sannan sai ya aza hannun sa na dama bisa saman goshin amaryar sa ya karanta wannan addu’ar:
‘Allahumma Inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi.’
Ita ma Amarya sai ta ɗora hannun ta saman goshin angon ta ta karanta kamar haka:
‘Allahumma inni as’aluka khairahu wa khaira ma jabaltahu alaihi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alaih.’
To daga nan sai su yi alwula su yi sallar nafila raka’a biyu á tare (watau cikin jam’i, ba daban daban ba),
In sun idar sai su yi kyawawan addu’o’in duk da ya kamata, su roƙi Allah Ya sa alheri cikin rayuwar auren su; Ya ba su zuriya ɗayyaba; ya ba su tsananin haƙurin zama da junan su, ya sa su kasance tare har a Aljanna maɗaukakiya, da sauran buƙatocin da suke fatan samu cikin rayuwar auren su.
To bayan nan, ana so su ɗan tattauna tsakanin su, kuma tattaunawa ta gaskiya da gaskiya ba tare da wani boye-boye ba,tun da dai an riga da an zama ɗaya.
Ango ya gaya wa amaryar sa dukkan irin abin da yake so da waɗanda ba ya so,misali ya ce: ‘Kin ga dai ni mutum ne da ba ya son raini, don haka ki yi kokayrin kiyaye dokoki na matuƙar ba su saba wa dokar addinin mu ba, sannan kuma ba na son yawan fita ba tare da kwakkwaran dalili ba.
A ɓangaren abinci ni mai son tuwo miyar taushe ne, ina kuma son fura da kindirmon nono,’ da dai sauran bayanai abin da yayi kama da waɗannan.
Haka ita ma amarya sai ta bayyana wa angon nata dukkanin abin da take so da waɗanda ba ta so, kuma su duka su yi niyya mai ƙarfi ta kiyaye haƙkin juna, don samun zamantakewa mai kyau, mai daɗi, wacce za ta iya fuskantar kowane yanayi na rayuwa ba tare da ginshiƙin ta ya girgiza ba ballantana har ya faɗi
Daga nan sai su karanta wani littafi na addini da ya yi magana a kan fiƙihun aure da ma’aurata, don su kara sanin haƙƙoki da irin nauyin da ya rataya a wuyan kowannen su. Ko kuma su samu wani faifai na wa’azin malamai a kan aure, su kalla ko suji tare suna masu tattauna abubuwan karuwa da suka ji a cikin sa.
Daga nan kuma sai a yi shirin kwanciya izuwa shinfiɗar barci. Yana da kyau sababbin ma’aurata su san cewa, ba lallai ba ne sai sun gabatar da ibadar aure a ranar farko.
Suna iya yin ƴan wasanni kaɗan kaɗan na nuna so da ƙauna, kuma inda za su maimaita hakan akalla kamar sau 7, ya zamar masu kamar wani ɗan kwas ne na fahimtar yanayin sha’awar juna, da kuma gane yanayin jikin juna da kuma gano malatsar sha’awar juna; in har za su iya wannan jinkirin, zai ƙara dandano, zimma da lazzar kayatarwar cikin ibadar su ta aure; haka kuma sai ta ƙara samun cika da fa’ida; domin in aka yi haka da wuya a samu matsala.
In ma an lura da matsala ana iya magance ta a wannan lokacin sanadiyyar wannan jinkirin.
Lokacin gabatarwar ibadar aure, ango sai ya daure ya bi a hankali da amaryar sa, domin zuciyar kowace sabuwar amarya cike take da tsoro da fargabar abin da ke shirin faruwa da ita a saduwar farko,
kuma zata iya ta ji tsananin zafi, don haka in ango ya bi ta a hankali zai iya rage mata wannan zafin da ruɗin da take ciki.
Gajiyawar sabon ango ko kuma muce kasawar sa,a ran daren farko ba abin fargaba ba ne,don shi ma yana cikin fargaba da tsananin ɗaukin yin wani abu a karo na farko wanda wannan na iya zauzautar da abubuwa a gare shi, don haka sai ma’aurata su sa haƙuri su ƙara gwadawa, su yi ta gwadawa har sai ango ya laƙanci abin sosai ya iya riƙe kansa har sai lokaci mafi dacewa.
Kuma kada amarya ta yi wa angon ta dariya dalilin wannan ko ta ce dama bai isa auren ba aka yi masa, ko ta ji haushin sa, sai dai ta kasance masoyiya kuma uwargida ta kwarai wacce ke tallafawa mijin ta a kowane lokaci.
Dole ango sai ya yi haƙuri da rashin taɓuka komai daga amaryar sa, kada ya ji haushin ta ko ya fara tunanin bai auri irin matar da yake so ba, mata suna da tsananin kunya ta ɓangaren bayyana jin lazzar sha’awar su, abin har ga matan da suka daɗe da aure, balle kuma sabuwar amarya!
Amma in ya yi niyya kuma, in har yana so,to cikin ƴan dabaru da fasaha da yawan yabo a hankali sai ya fitar da kunyar nan daga gare ta har ta riƙa yin irin yadda yake so.
Amarya kuma ta sani cewa in ta daure ta, ta fara cire kunya tun a ranar daren farko ya fi alheri a gare ta da ɗaurewar farin ciki a rayuwar auren ta.
Kafin gabatar da ibadar aure, yana da kyau ga sababbin ma’aurata su san dukkan ƙa’idojin ibadar aure, kuma su tanadi dukkan abin da ya kamata su tanada.
Muna fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawar Sa a koda yaushe, ameen.