Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Kano a ranar Litinin kamar yadda aka tsara Gwamna Abdullahi Ganduje dai ya nemi Buhari ya dakatar da zuwansa jihar saboda wasu dalilai da abun da zuwansa ka iya haifarwa An tattaro cewa shugaban kasar zai je ya kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin tarayya a jihar ta arewa 

Duk da adawar da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya nuna kan haka, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya ziyartan jihar a gobe Litinin, 30 ga watan Janairu kamar yadda aka tsara, Nigerian Tribune ta rahoto. Bincike sun nuna cewa shugaban kasar bai girgiza da hujjar da gwamnatin Kano ta kawo ba na son a dage ziyarar da zai kai jihar. 

A wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a gidan gwamnatin Kano wanda ya samu halartan malamai, yan majalisa, shugabannin siyasa da yan kasuwa, Ganduje ya bayyana shawarar da suka yanke na neman shugaban kasar ya dakatar da ziyararsa. 

Gwamnan ya bayyana cewa jihar ta damu matuka da mawuyacin halin da jama’a ke ciki game da sauya tsaffin kudi, rahoton The Cable 

Ya ce an yanke shawarar ne don gudun duk wasu abubuwa da ka iya kaiwa ya komo. Hakazalika, gwamnatin jihar ta aike wasika zuwa ga shugaban kasar tana sanar da shi dalilan da yasa ziyarar da yake shirin kaiwa bai kamata ba a wannan lokaci. A cewar wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren labaran gwamnan ya saki, masu ruwa da tsaki a jihar sun goyi bayan hukuncin shawartan shugaban kasar kan kin kawo ziyara jihar. 
Previous Post Next Post