Karancin sabbin kudi yana cigaba da janyo karuwar masu kasuwancin sabbin kudin kan farashi mai tsadar gaske a gari Bincike sun nuna yadda wasu masu tallar sabbin kudi a tashar motar Dadi na Sabon Garin Zaria da ke jihar Kaduna suka yi dandazo a gefen babban titin suna tallata hajarsu An tattaro yadda a yanzu suke siyar da bandir din 'yan N200 kan N30,000; bandir din 'yan N500 kan N70,000 da kuma bandir din 'yan N1000 kan N130,000 

Zaria, Kaduna - Ana tsaka da karancin sabbin kudi, masu tallar sabbin kudin da aka canza sun cika tashar motar Dadi da ke karamar hukumar Sabon Garin Zaria da ke jihar Kaduna. 

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, wadannan masu tallar suna siyar da sabbin kudi kan farashi mai tsadar gaske. 

Babban bankin Najeriya ya tsaya kan bakarsa na cewa babu gudu ba ja da baya kan wa'adin daina amsar tsoffin kudi. Bincike ya bayyana yadda masu tallar sabbin kudi daban-daban daga bandir din 'yan N100 da suke saidawa kan N16,000, N200 wanda suke siyarwa N30,000 duk bandir daya; bandir din N500 kan N70,000 yayin da suke siyar da bandir din N1000 kan N130,000. 


Previous Post Next Post