Babban bankin kasa CBN, ya umarci bankunan kasuwancin kasar nan da su daina bayar da sabbin kudade akan kanta, sai dai a injinun cirar kudi na ATM. Dakar sannan ta kara jaddadawa bankunan kan su kiyaye da umarnin tare da aiwatar da shi a hada-hadar kudi.
Yace hukumomin gudanarwar bankin sun gano cewa akwai korafe-korafe daga yan Nigeria kan yadda sabbin kudin suka ki zagayawa a tsakaninsu, alhalin sun kusan kwana ashirin da sakinsu.
Mai magana da yawun bankin ya ce dokar an bayar da ita ne dan kara sakin kudin da kuma kara yawan zagaya kudin kafin wa'adin kare amfani da tsoffin yayi a ranar 29 ga wannan watan.