FCT, Abuja - Wani mutum mazaunin birnin tarayya Abuja dan shekara 63 da ke sana'ar panel beater, Taiwo Ojo ya shiga hannun yan sanda kan kashe abokin aikinsa. An kama Ojo ne saboda zarginsa da kashe abokin aikinsa mai suna Philip Kura, ya kona gawarsa ya kuma birne shi a wani kabari mara zurfi a Bwari, da ke birnin tarayya Abuja, rahoton The Punch.

Daily Post ta rahoto cewa Ojo ya halaka abokin aikinsa ne saboda jayayya da suka yi kan wani kudi a ranar 23 ga watan Disamba, kamar yadda wata majiya na bayanin sirri ta bayyana.
Previous Post Next Post