‘Dan wasan gaba na kasar Faransa Kylian Mbappe ya kafa wani sabon tarihi na jefa kwallaye 3 a wasan karshe na cin kofin duniya, abinda ya kai yawan kwallayen da ya jefa a gasar da aka kammala a Qatar zuwa 8.
1962 da Pele a shekarar 1958 da 1970, sai Paul Breitner a shekarar 1974 da 1982 sannan Zinedine Zidane a shekarar 1998 da 2006.
A shekaru 23 Mbappe ya jefa kwallaye 15 a gasar cin kofin duniya a wasanni 17 da ya buga, wadanda suka zarce na zaratán ‘yan wasan Faransa irinsu Thierry Henry mai kwallaye 6 da Zinedine Zidane mai 5.
Ya zuwa yanzu ‘dan wasan Jamus Miroslav Klose ke rike da tarihin jefa kwallayen da suka fi yawa wadanda suka kai 16 a gasa 4 da ya halarta.