Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, kalli budurwar da Tasha Guba saboda saurayinta yaki kulata.
Wannan budurwa da kuke gani sunanta Maryam haifaffiyar kauyen Dakatsalle dake jihar Niger, Kuma allah ya jarabceta da son wani Matashi me suna Aliyu, sai dai kuma shi Aliyu ya tsani ayi Masa maganar ta saboda tsanarta da yayi.
Kullum Maryam takanje takanas har gidan su Aliyu domin gaida mahaifansa duk da cewa tasan wannan abin da takeyi ko a kafar takamasa baya gani Amma hakan Nan take jurewa Tana zuwa kullum,
Aliyu yasha tarar Maryam ya doketa ko Mari akan tadena zuwa gidansu Amma hakan baisa ta sauya halin nata ba.
Wata Rana Maryam ta fito zataje kasuwa sayen kayan Miya, mamanta ta aiketa aikuwa sai taga aliyu a hanya tare da abokansa, Nan take taje ta gaida abokan aliyu Amma shi ko daga Kai baiyi ba bare ya kalleta, haka ta wuce ta tafi aikenta, duk da cewa abinda Aliyu yayi Mata bataji dadinsa ba, haka ta dawo gida ta rasa me yakeyi Mata dadi Tana kuka, mamanta ta tambayeta me yake damunta Amma kawai Maryam ta Shiga daki Tana wannan kukan Bata gaya Mata ba.
Chan Maryam tana wannan dakin Tana kuka sai taga ai ba amfanin zamanta a duniya muddin Aliyu bazai kulata ba, ai kuwa Nan take ta dauki kwalbar Fiya-Fiya maganin kwari Tasha domin kawai ta mutu kowa ma yahuta, chan sai mamanta taji alamun ana motsi a dakin kamar ba lafiya, kawai sai ta rinka Kiran sunanta, Maryam..Maryam...Maryam... Har sau uku Amma shiru kakeji, Nan take ta nufi dakin, zuwanta keda wuya taga Maryam a cikin wani mawuyacin yanayi, inda take futar da yawu ta Baki da ta hanci, maman Maryam batayi kasa a guiwa ba ta futa waje da gudu Tana kuka, Tana nemam taimakon makota, Nan aka hadu makil a kofar gidan su Maryam aka dauketa a mota aka kaita asibiti.
Bayan an kaita asibiti kwana biyu Bata farka ba likita yace sai anyi Mata aiki domin gano abinda yake damunta, sai sukace to ayi Mata, Allah ya bada sa'a,
Sai aka Shiga akayi Mata aiki aka gano duka Koda ta guda biyu ta samu matsala Kuma zata iya rasa ranta idan har ba'a samu ta Wanda za'a saka Mata ba a cikin kwana biyu, aikuwa Nan akai ta gwada ta 'yan uwa Amma batayi ba.
Chan sai kawayen Maryam sukaje suka samu Aliyu suka gaya Masa abinda yake faruwa da Maryam, ai kuwa hankalinsa yayi matukar tashi, yayi sauri yaje asibitin Yana kuka, Wanda zuwansa din yabawa kowa mamaki.
Bayan kwana Daya dai ba'a samu Wanda Koda sa yayiwa Maryam daidai ba gashi Kuma likita yace idan ta kwana biyu a haka zata iya rasa rayuwar ta, Aikuwa Nan take Aliyu yace to a gwada tashi Mana ko zatayi, sai kuwa aka Shiga da aliyu dakin gwaji, cikin nasara likita yace kodar aliyu yayi daidai data Maryam, aka Shiga akayi aiki a cikin nasara, Kuma Maryam ta samu lafiya sumul, abin burgewa Kuma Aliyu yaje har gida Yaba Maryam hakuri akan abubuwan da suka faru a baya ya bayyana Mata Kuma yana sonta, Nan take itama ta amince akayi musu baiko, saura Saurin aure.
Allah yayi Mana tsari daga fadawa makauniyar soyayya.