An saki Matashi Aminu Muhammad Wanda yayi kalaman Batanci ga uwar gidan shugaban kasa First lady Aisha Buhari
Idan me sauraro be manta ba a 'yan kwanakin nan ne aka samu wani matsahi Dalibin jami'a yayi rubutun Batanci akan uwar gidan shugaban kasar Nigeria muhammadu Buhari, inda labarin yaja hankali a kafafen sada zumunta na social media, Har kowa ya rinka fadar albarkacin bakinsa, inda wasu suke ganin abinda matar shugaban kasar tayi yayi daidai, wasu Kuma suke ganin batayi daidai ba sakamakon Rashin bin doka datayi wajen Kama aminu.
Yanzu dai magana ta Kare inda yanzu haka an saka aminu Muhammad, yayin da alkalin aminu Muhammad din yake shaidawa shafin BBC HAUSA, Kuma Aisha Buhari ta bukaci al'ummah suyi hakuri akan wannan Abu daya faru.