Tsohuwar fitacciyar Jarumar Kannywood Kubura Dako tana ɗaya daga cikin manyan jaruman Kannywood wanda sukayi tashe a shekarun baya kamar babu gobe,sunyi shura sama da ta Rahama Sadau balle kuma su Hadiza Gabon ko Maryam Yahaya.

Tsohuwar Jarumar ta fito a manyan finafinai daga shekarar 2004 zuwa 2010,ga wasu daga cikin finafinan;

Gata

Tutar so

Fati yar Adamawa

Taron dangi

Hausa bakwai

Dare da yawa

Tun bayan ɓullar wani fefen bidiyon Jarumar a shekarun ta bar masana’antar aka dena ganin ta,wanda ko labarin ta aka dena ji wanda hakan yake da nasaba da ƙasar data bari ta koma kasar Malaysia, mun ji labarin cewa ta kammala karatun ta da takeyi a kasar (Sociology ) sannan tayi service dinta a federal ministry of agriculture area 11 dake garin Abuja.

Kwatsam a shekarar 2019 wani hoton ta ya bayyana, wanda aka ganta cikin wata shiga data saɓa da al’adar Malam Bahaushe wanda akayi ca akan hotunan na ta a wannan lokacin.Tun daga lokacin har yau ba’a jin ɗuriyar tsohuwar Jarumar.Halin da Jarumar take cikiA wani bincike da Labarai.com.ng mukayi,mun gano Jarumar bayan barin ta daga ƙasar Malaysia zuwa Najeriya.Jarumar ta gamu da wani iftila’i na matsalar kwakwalwa wanda daga bisani ta dinga zuwa Asibiti domin duba ta wanda daga karshe a yanzu haka tana gidan iyayen ta dake jihar Neja kamar yadda wasu maƙotan su suka bayyana mana.Yanzu haka tana ƙara samun sauƙi.Muna rokon Allah ya bata lafiya Amin.
Previous Post Next Post