“Muka yi ta kiran lambar ɗan sa-kai ɗin da ya kira mu, amma bai amsa ba. Sai muka tafi ofishin su.”
Ya ce a can shi da kawun sa an kulle su, sannan aka tilasta su laƙa wa mahaifin sa sharrin cewa ya na da alaƙa da ‘yan bindiga.
Sanata Marafa Ya Yi Barazanar Ɗaukar Mataki:
Jigon APC a yankin, Kabiru Marafa, ya sha alwashin ɗaukar mataki dangane da kisan Lawali, wanda makusancin sa ne.
Marafa ƙanin Sarkin ‘Yandoto ne, Aliyu Marafa. Marigayi Lawali ɗan siyasar karkara ne, wanda ke da kurɗa-kurɗa a cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Tsohon Sanata Marafa ya shaida wa ‘yan jarida a Gusau a ranar Talata cewa zai maka waɗanda ake zargi da yin kisan a kotu, dangane da kisan gillar da suka yi ba bisa tuhumar sa kamar yadda kotu ta tanadar ba. Ya ce zai saurara har sai an fitar da binciken likitoci tukunna.
“Su biyun, wato Lawali da ɗaya mamacin an gallaza masu azaba ne har ran su ya fita. Na ukun ya tsira da raunuka a kafaɗun sa. Mai yiwuwa Magaji ya mutu saboda raunuka da dama da aka yi masa a ɓangaren jikin sa na hagu.
“Ya zubar da jini ta idanun sa, hanci da baki. Mun kuma lura da jini a fuskar sa. Zan bibiyi wannan kisa da aka yi har ranar hukunci a kotu,” cewar Marafa.
Ya shaida wa manema labarai cewa DPO na ‘yan sandan Tsafe ya shaida masa cewa ba shi da masaniyar ‘yan sa-kai sun kama Lawali.
Wakilin mu ya tuntuɓi Kwamandan ‘Yan Sa-kai, Rabi’u ‘Yandoto, kuma ya ce gwamnatin Zamfara na binciken lamarin.
Yayin da ya ce Gwamnatin Zamfara na binciken gano waɗands suka aikata kisan, a ɗaya gefe kuma ya shaida wa wakilin mu cewa mai yiwuwa ba jami’an Sa-kai na CPG ne suka kashe shi ba.
Rabi’u ‘Yandoto wanda tsohon Laftanar Kanar ne, ya ce ba a bai wa jami’in CPG ko ɗaya iznin zuwa kamo ko mutum ɗaya ba, ballanata ya ɗauki doka a hannun sa.