kwantiragi, domin ya samu ya ciyar da iyalin sa, kuma ya ci gaba da biyan kuɗin makarantar ‘ya’yan sa biyu.
Ita kan ta matar ta sa ba ta da lafiya a ranar da ya fita aka sace shi. Domin ko rakiya ba ta iya fita ta yi masa ba zuwa inda zai hau mota zuwa tasha.
Matar sa ta yi zargin ‘yan ‘One Chance’ ne suka sace shi a cikin mota a lokacin da ya bar gida kafin a kai tashar Jabi.
An yi ta tattauna wannan batu a soshiyal midiya, har lamarin ya yi tsami sosai.
Matar dai ta ce sai ranar Lahadi da rana ‘yan bindiga su ka kira ta, suka ce sun yi garkuwa da mijin ta, amma su na buƙatar Naira miliyan 100 kafin su sake shi.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan FCT Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa wakilin mu cewa ta na cikin wani taro, za ta kira idan ta fito. Amma dai har yau ba ta kira ba.