Masu zanga-zangar nuna goyon-bayan Falasdinawa sun karade manyan birane Landan domin neman duniya tayi adalci kan luguden wutar da ake yi a Gaza.
Wadannan masu zanga-zanga a birnin Landan ba wai asalin Falasdinawa ba ne kadai, akwai musulmai daga kasashe daban-daban mazaunan wannan kasa, da ke nuna goyon-baya da takaicin kisan da ake yi wa Falasdinawa fararen hula.
Masu zanga-zangar dai na zargin Burtaniya da kawayenta da nuna goyon baya ga Isra’ila a fadan da aka kwashe fiye da mako daya ana gwabazawa.
Ahmad Ghassan na daya daga cikin masu zanga-zangar. Ya ce “Ba za mu kira abin da ke faruwa da sunan rikici ba, sai dai muna son duniya ta san cewa, kokari ne na karbe abin da tun asali namu ne, duk da cewa kasashen duniya da dama har da manyan kafafen yada labarai na sukar Falasdinu har nan Brutaniya, Firaiminista Rishi Sunak bai ce uffan kan halin da Falasdinu ke ciki ba, to shi ya sa mu muka zabi mu fito mu sanar wa duniya cewa, a shirye muke mu yi wannan fafutukar kwatarwa kanmu ‘yanci ba tare da mun bata lokaci ba’’
Aman Ayoub dan kasar Bangladesh ne, da ke da ra’ayin cewa, tura ce ta kai bango, saboda haka bai wa Falasdinu ‘yancin zama kasa mai cin gashin kanta ne kawai mafita a wannan tashin hankalin.
”Na shiga wannan zanga-zangar ta lumana domin jan hankalin duniya domin a dakatar da fadan da ake yi tsakanin Isra’ila da Falasdinu, ana ta kashe mutanen da ba su ji ba-ba su gani ba, ana gallazawa mutane azaba da jefa rayuwarsu cikin ukuba, laifi dadai da kisan kiyashi ake aikatawa, don haka muka fito muna neman a kawo karshen rikicin tare da bai wa Falasdinu ‘yancin zama kasa mai cin gashin kanta’’
A gefe guda kuma, suma wasu Yahudawan Isra’ila sun yi tasu zanga-zangar lumanan a yammacin jiya Lahadi a kusa da ginin majalisar Burtaniya domin nuna takaici da neman sakin wasu mutane da suka ce ana garkame da su sakamakon wannan rikici.
Isra’ila na ci gaba da nanata cewa ba zata raga a wannan yaki ba, har sai ta ga bayan Hamas duk da yanayi na muni