DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani mutum da shan ruwansa bai ƙare ba, ya samu nasarar ceto shi a cikin teku bayan ya shafe kimanin sati biyu ya na galudaya ba tare da sanin makomar rayuwarsa ba.
A cewar Steve Strohmaer, mai kula da gaɓar tekun da ke yankin Washington, sun samu saƙo ne daga wasu masunta cewar sun hango wani mutum ya na iyo a cikin ruwa. Daganan suka garzaya da kayan aiki don zuwa su ceto shi.
Sai dai ya bayyana cewar bayan sun gama bincike akan mutumin sai suka fahimci ɗaya ne daga cikin mutane biyu da aka kawo musu rahoton sun ɓace a cikin tekun kimanin sati biyu da suka shuɗe. Wanda hakan ba ƙaramin abin mamaki ba ne.
Jaridar Kano Times ta rawaito cewar mutanen biyu masu yawon kamun kifi, sun shiga tekun ranar 12 ga watan Oktoban shekarar nan, kuma ana sa ran za su dawo bakin gaɓar ruwa ranar 15 ga wata. To amma sama da sati biyu shiru ba labarinsu.
Mr. Steve ya ce tuni suka garzaya da mutumin asibiti don duba lafiyarsa, sannan idan sun gama yi masa tambayoyi za su yi ƙoƙarin ganin sun tafi ceto abokin tafiyar ta sa.
A wani labarin kuma Kano na kan gaba a Wajan masu kamuwa da cutar Mashaƙo -NCDC
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.