Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta kame shugaban jam'iyar PNDS mai mulkin kasar
Rahotannin da ke zuwa daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa sojojin da suka yi juyin Mulki a a kasar sun kama shugaban jam'iyar PNDS Tarayya Foumakoye Gado, babban wakilin shugaban kasa, da kuma ministan man fetur Sani Issoufou Mahamadou a wannan Litinin.
Wallafawa ranar:

Hakan na zuwa ne bayan dakatar da tsohon ministan tsaron kasa kuma dan majalisa, Kalla Moutari, wanda aka kama tun a ranar Alhamis da ta gabata .
Babu dai wani Karin bayani a game da dalilan kama su, amma shi Foumakoye Gado a matsayinsa na shugaban jam'iyar PNDS Tarayya ya rubuta takarda, inda ya bukaci rassan jam'iyar su gudanar da zanga-zanga da yin sanarwai na kiran a tilasta wa sojoji su saki shugaba Bazoum.
Foumakoye ya yi hakan ne duk da sojojin Sun dau matakin dakatar da ayyukan jam'iyun siyasa.
A ranar Larabar da ta gabata ne dakarun tsaron lafiyar shugaban Nijar suka yi garkuwa da shugaba Bazoum Mohamed, abin da yaa kai ga juyin mulki.
Kasashen duniya da kungiyoyi sun yi ta mayar damaartani a kan wanna al’amari, inda ma kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta bai wa sojojin da suka kifar da gwamnatin wa’adin mako guda su maido da shugaba Bazoum ko ta dau mataki a kansu.