Ayyiriri! Cikin yardar mai duka a yau aka daura Auren fitacciyar jarumar Kannywood dinnan Maimuna wadda akafi sani da Mommy Gombe,wato wadda ta fito a wakar Jarumar Mata ta Hamisu Breaker da dai sauran shahararrun wakoki da finafinai.
Labarin ya fita ne a yau,bayan ganin mai gidan ta wanda ya fito da ita a Kannywood,Sunusi Oscar ya wallafa hoton su tare gami da yi mata addu’ar Allah ya sanya Alkairi da kuma fatan mutu ka raba.
Bayan ganin wallafar keda wuya sai muka leka shafin jarumar:ta haska inda ake bikin nata ake raye rayen Fulani,sai kuma inda ake mata kwalliya a yau tana dab da shiga ciki.
Muna rokon Allah ya basu zaman lafiya.
Ga bidiyon shagalin da kwalliyar Amarya Mommy Gombe din anan kasa.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan kun karanata wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.