Uwargida, idan dai har kin gane cewa yanayin jikin ki ba lafiya lau yake ba ta bangaren kula da gadon ki, to yanzu dai dama ce ta sameki cikin sauki akan matsalar data shafi gyaran kai da jiki a rayuwar aure tsakanin ki da mijinki.
Ta wannan hanyar ne kadai zaki samu damar yin yadda kike so da kuma karkato da akalar maigida yayi dukkan abinda kike bukata, matukar idan dai ya dandana ki zaiji kin gamsar dashi yadda yake so.
Wannan sirrin na alkama shi kadai idan dai an rike shi dakyau za’a ga abin mamaki dangane sakamakon da yake haifar wa. Dalilin kuwa shine mata da yawa sun jarraba shi kuma sunga alfanun dake tattare dashi.
Abubuwan da za’a nema wajen hada wannan sirri:
Alkama
Nono
Ruwan dumi
Garin alkama na daga cikin nau’o’in abincin da ma’aurata ke bukata wajen karin ni’imar aure.
Yadda ake sarrafa shi kuwa shi ne:
Ana samun garin alkama a hada shi da nono mai kyau, ko madarar shanu, wadda aka tatsa yanzu-yanzu, a rinka hadawa da ruwan dumi ana sha.
Hakan yana magani sosai wajen mu’amala tsakanin mata da miji, musamman kara dadewa a yayin jima’i.
Allah yasa mudace.