MASU FAMA DA CHIWON HANTA GA MAGANI FISABILILLAH,
Duk wanda yake fama da chiwon hanta ya gwada wannan maganin da temakon Allah za’a dace,
Kasamu albasa wato onion guda shida 6 manya sannan ka yayyanka su kamar za’ayi miya,
Sai kasamu ruwa wato water galon daya five litre 5 sai ka raba ruwan gida biyu, sai ka dauki rabin ruwan wato half galon sai ka dafa albasar onion da rabin ruwan,
Bayan ka gama dafa albasar onion sai ka tache albasar sai ka zubar da albasar, sannan sai ka dauko rabin ruwan daka ware sai ka hada shi da rabin daka dafa albasar kaga ya dawo galon guda kenan,
Sai ka samu zuma mai kyawu, sai kasamu karamin kofi irin na silver ko kuma karamin kofin roba,
Sai ka rinka chika small cup din, sai ka dibi zuma chokali uku ka saka a chikin small cup din, kana sha sau uku arana har sai ruwan ya kare da zuman,
Bayan ka gama kaje asiviti ka yi gwaji insha Allah za’a samu waraka da yadda Allah, Allah yasa adace,
‘Yan uwa zaku iya share ko copies na wannan rubutun Domin al’umma su amfana dashi,
1. Gab da kafin kaci abinci karka sha ruwa.
2. Bayan Gama cin abinci karka sha ruwa nan take sai bayan kamar minti 15, sannan duk kasalar da zakaji karka kwanta irin wannan lokacin
3. In zakai ibadar aure gab da yi karka sha ruwa, bayan gamawa kada kasha ruwa nan da nan, sai bayan mintoci kusan 15 zuwa 20
4. Kar kuma ka auka bandaki da niyyar Wankan tsarki bayan Gama ibadar nan da nan, a’a kadan jira tukun
5. Gab da zaka shiga bandaki Wanka ko fitsari nan ma karka sha ruwa, Bayan ka fito nan ma karka sha ruwa nan da nan.
Insha Allahu in aka kiyaye wannan za’ai lafiyar jiki kwarai da gaske.
Kuma koda kana fuskantar matsalar nan ta riƙa jin bayan kagama fitsari ka miƙe wani ɗan kaɗan na fitsarin na zubowa ya ɓata maka wando, ko wasiwasi haka kurum bama fitsarin kai ba amma ka riƙajin kamar wani ya fito ta gabanka, ko ya zamto ka riƙa jin kamar maziyi ya fito ma alhalin inka duba zakaga bakomi.
Toh inde ka kiyaye wadancan tips din insha Allahu zaka dena walau Mace ko Namiji.
[Ibrahim Y. Yusuf]
TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA’I A ZAMANIN YAU
●••••○•••••●•••••○•••••●•••••○•••••●••••
Bayani ne mai nauyin gaske da kuma ke kunshe da dunqulallun bayanai masu mahimmanci. kamar yadda na alkawarta abaya zanyi!
Toh saide da farko zan fara da cewa; gaskiya idan kasan ko kinsan bakya iya tsayawa ku karanta dogon post a natse komi mahimmancinsa toh ina rokonka dakai gaba kurum, domin post din me tsayi ne kwarai, ahakan ma na takaita shine bakuma nason rabashi saboda hakan zai iya sa wani parts din ya zamo missing… saika karancesa zaka fahimcesa da kyau….
Amma nayi BOLD HEADLINES da paragraph aciki da zaka iya fahimtar inda ka tsaya koda baka karancesa lokaci daya ba.
Hakika rayuwa da kuma zamani sun canza takai ga wasu abubuwan da ada ake lullu6esu ayau sun fito fili har sunfara zamowa bakomi ba. Da yawa mutane basu dauki tattaunawa game da irin wadannan ke6antattun al’amura na jima’i wani abu ba musamman atsakanin sa’oin juna, abokai ko kawaye maza da mata.
Mata basa jin kunya su zauna tsakaninsu ko wani group-group suna tattaunawa game da yadda mazajensu ke saduwa dasu, subahanallah. Haka ma cikin Mazan… duk da ansan wannan bai daga cikin tarbiya ta musulunci.
Toh saide nisara yacimu da yaki kuma dama Annabi ya fadamana inde muka daukesu ababen koyi toh Koda zina suka dawo yi agefen titi muma ana nan wataran sai mun fara jaraba hakan……
::::::::::::::::::::::~~~~~●~~~~~::::::::::::::::::
SHIN TAYA SUKA CIMU DA YAKIN ??
Anci mu da yaki ne ta hanyar kafofin internet da social media dake yaďa batsa da alfasha barkatai a waya da mutum zai hau internet ya danna ya shiga shafin da duk yakeso ya kalla ko takalli duk irin abunda takeso na jima’i da rashin kyautawa, wanda kaso mafi yawa sun bude ido dasu ayau har kuwa da masu aure cikin masu bibiyar irin wadannan shafuka wanda hakan ya canza tunanin alumma daga fuskantar gaskiya zuwa karya.
Sannan kuma uwa uba ga group-group na batsa a social media da haka kurum yaro ko yarinya zasu zauna su tsara batsa zallah sui posting kaga wacce ko aure batai ba amma ta zage tana bayanin yadda ake kwanciya…
ko kuma bayani yadda kaza ya kasance tsakanin wane da budurwarsa wance haka kurum kirkirarrun labarai na banza da wofi da mutum me cikakken hankali bazai dauka ba…..
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Toh amma kasan dake kwakwalwa wawuyace, sannan wasu tunaninsu bai wuce saman gashin kansu… wadancan rubututtuka da suke karantawa tare da videos da suke kallah duk sai su aransu lallai fa hakan ce ta faru… don haka nima ya zanyi nai kaza dinnan ko kuwa in Mace ce ya akai mijina bai mun kaza dinnan gaskiya yana cutata kenan.
Wanda dalilin hakan kesa sakararru cikin Matasan mu su bazama neman maganin gaba batare dafa yaje wajen likita andubasa an tabbatar baida lfy ba! A’ah kurum shine tunda yaji anqaga labari kan abunda baya iyayi toh kurum ya lamincewa kansa dole yana da bukatar magani shima baida lfy…
Hakan yasa gashinan matasan mu shekara 20 zuwa 45 nata faman fankan-fankan suna shan magungunan hausa dana turawa alhalin lafiyarsu kalau, raina wuya sukai sukaje kaa adalilin kallo da karatun abubuwan da gidadancinsu ne ya kaisa garesu… karshe har shaye-shayen magungunan ya haddasa masa matsalar da ada bashi da itan.
Ko kuma wani kurum ya kawoma labarin maganin jima’i ka hau sha alhalin kalau kake kasani wai kai zakaiwa kanka service. Ai ba service sama da samun hutu, isashshen bacci da abinci me kyau. Abun haushi wasu nashan wadannan magungunan ne domin aikata zinace-zinace.
Hakama ciki MATA zakaga mace na zaune lafiya amma karatun batsa yasa ta fara ganin kasawar mijinta harta dena jin gamsuwar da take samu dashi, saboda taga video ko labarin da bakomi sai karya, rashin kangado da juya lafiyayyen tunani….Kaji ana anyima wata hawa yakai 3 zuwa 5 tana inzali kamar famfo….
Wanda kuma in ba’ai muwafaqa ba daga hakan mace tunda ta raina mijinta kome yai bazata gani ba don haka saita fara tunanin ina zata samu ta shigo da namiji wanda kafin a farga shikenan ta zama mazinaciya…
Kuma mafi illar intaji duk mazan basui daidai da curiosity din da ta karanta ba akarshe tana karanta labaran jima’i harda na madigo dan haka saita fara tunanin jarraba neman mace yar uwarta wanda ta wannan hanyar yau Allah kadai yasan matan auren da suke madigo. Za kaga Miji na can wajen neman halak, matarsa ta kawo ko ta tafi wajen wata na suna alfasha saboda iskanci da rashin ganin girma Allah da manzonsa.
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Don haka adalilin finafinai da posts na batsa da maza da mata ke ta ammali dasu yasa cikin mutanen mu duk sun raina lafiyar kansu alhalin kalau suke wanda hakan ke nuna kalle-kallen finafinan batasan da karanta labarurrukan batsa ya soma haddasa musu larurar kwakwalwa ta SEXUAL AVERSION DISORDER ko OCD wacce wataran inba Allah ya kiyaye ba tohfa bama kasa zama ko rike aure ba abunda zai sameku kila sai andaure mutum, domin zai shiga abubuwan da matar saita gudu…. Gashi nan Allah kadai yasan masu saduwa ta dubura kurum tsit matan suke, da masu turamusu abubuwa iri-iri a farji… kuma ana nan depression zai gama da mutum.
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Yaku Matasan mu Mata da Maza kusani finafinan batsa ba gaskiya bane. Fantasies ne kurum, wani girman size din gaban namiji da za’a nuna duk prosthesis ne kamar yadda suke hada Dildo suna halakar da matan mu ayau kaga sample din gaban namiji sak to suma hakan ake basu penis implant me laushin dake sajewa da fata wanda bazaku iya tantancewa ba kuzo kuna raina abunda Allah ya baku wanda a zahiri ma naku yafi nasu…
Haka nan maniyyin da zakuga ana fitarwa yana tsartuwa a irin wadannan clips din duk FAKE ne wallahi ba maniyyi bane na gaske… Kirkirarren solutions ne da ake hadawa da spunks da methilcellulose…
Sannan abunda ke faruwa yadda kuke ganin igiyar karin ruwa da ake sawa mara lafiya ahannu… haka ake zura wannan igiyar bututun ta cikin PENIS implant din ya biyo kasan matsematsin namijin ya saje da fata bazaku iya ganin ingiyar tube din ba… don haka me kwantrol din yana daga baya rike da katon siringi irin 60ml din ya zuqi kirkirarren farin maniyyi din iyakaci in sun nuna muku kamar anagama saduwa sai director din ya bada umarnin me rike syringe din ya danno maniyyin sai kuga abu yana tsartuwa ku dauka ajikinsa yake fita….
Wanda wannan abun shikesa wasu matan su rika ganin mijinsu kamar bashi da lafiya… ko shi namijin saboda sakarci ya rika wai baya fitar da ruwan maniyyi sosai ya raina kansa. Shiyasa galibi tambayar farko da nakewa irin wadannan in sunce mun wai suna da karancin ruwan mani itace ta ya kagane baka fitar da maniyyi sosai? Me ya nuna ma hakan? Ko kuma ma na share mutum…. domin akwai shirme kila mutum ya haihu ya qara yiwa mace ciki amma wai yana batun karancin maniyyi… kana da karancin maniyyin zaka iyama mace ciki? Da munji haka munsan inda ka samo wannan tunanin…
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Sannan MATA babu wani abu wai shi Release a mace da kuke gani ana haska muku ko kuke karantawa a posts marasa tsafta wai mace ta kawo tana tsartuwa maniyyinta kamar zai ta6o saman ceiling daki… Karyar banza ce.
Abunda ake nufi da Orgasm din mace shine gamsuwar ita akaran kanta ne aranta cikin kwakwalwarta zataji ta gamsu kuma intai irin wannan jikinta ne mneke saki kamar yadda namiji inyai inzali zaiji sha’awa ta qare masa….
Akwai wani abu daga cikin cuttukan jima’i da ake kira UROPHILIA wanda abokin jima’i ke sha’awa yin fitsari jikin daya yayin jima’i abunda kan samesu kenan ku rika zaton maniyyi mace ke fitarwa fitsari ne.. sai kuma irin Artificial lubricates da ake samusu ta syringe suma adanna ku zaci wai release suke.
Za aima yara aure kaji mace tazo tana ita de tana saduwa amma bata ta6a ganin tai release ba… inajin wannan suma nasan inda suka dauko wannan gurbataccen tunanin… karatun post din batsa ne. Eh gaban mace yakan jike yai damshi saboda glands amma babu wani abu wai Release ko inzali a mata. Don haka kaima sakaran namiji dake jiran wai kaga matarka tai release kasani babu wannan abun baza kuma ka ta6a gani ba.
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Sannan sakamakon ganin irin wadancan abubuwa na girman size din azzakarin porn stars sai kaji namiji yazoma wai yana fama da kankantar gaba. Shi gabansa ba tsayi, wanda galibi inka binkicesu normal size garesu… kurum low self esteem ne ke damunsu. Eh anji wani azzakarinsa yafi na wani tsayi da kauri amma hakan bashike nuna kaima naka yana da matsala ba….
Sannan mutum xaizo yana takaici duk depression ya damesa wai baya iya jimawa a jima’i minti 5 yake kawowa… kuma gashi lafiya kalau rayuwar aurensa yana da sha’awa wanda abunda ke nunawa shine kila mutum ya kasance mai kallon finafinan batsa yana ganin video na minti 10 zuwa 40 ko sama duk kuma a nuna mutum daya ke jima’i. Don haka shi mai yin minti 5 sai ya fara sawa ransa cewa lallai toh baida lafiya.
Wanda kuma nafada muku duk karyace wancan videon babu wani jima’i irin wannan kamar yadda nace muku delusion ne ku kuke ganin jima’i amma ba gaskiya bane kaso 60% na abunda kuke gani FAKE ne.
Abunda nakeso kusani eh akwai wasu larurorin dake hana samun sha’awa kamar karancin sinadaran jima’i, larurar kunci da fargaba wato anxiety/depression. Sannan musamman depression yana iya haddasa saurin inzali,
Haka kuma inde halinka ne masturbation toh dama ka qulla abota da saurin inzali, inkai wasa ko kafin kake cire kayanka zaka iya kawowa ma kan ka ta6a macen domin ka birkita kwakwalwarka ta yadda tuni take fara jima’in kafin jikinka ya fara… kuma shyasa ko aure sukai suke samun matsala.
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~
Sannan wani girman breast da kuke gani a irin wadannan finafinan duk SILICONE implant ne ba NATURAL bane aiki ake asamusu, shaysa har cikin maza transgender wato yan daudu cikin turawa suma zakuke ganinsu da nonuwa…
Inkace wai kayi amarya kuma haka kake tsammani kaga mace budurwa irin tamu da irin wannan nonon na video toh a gaskiya ina jajantama domin ka HAUKACE.