KARIN AURE ALHERI NE
Magidanta masu mata daya wanda suka ki kara aure alhali suna da lafiya da rufin asiri to ba shakka suna bada gudumawa wajen yawaitar aikata fasadi tsakanin al’ummah
A wannan lokacin, ya kusa ya zama wajibi ga masu mata daya su kara aure, kai mai mata daya ka sani akwai daruruwan matan da suka rasa mazajen aure, saboda mazan sunyi karanci
Idan akace kowani namiji ya takaita da mata daya alhali matan sun ninka mazan yawa kusan sau biyar, to sauran matan wa zai aure su kenan?
Rashin kara aure yana haifar da kowani irin fasikanci da fasadi a tsakanin al’ummah, bincike ne ya tabbatar da hakan
Ke kuma baiwar Allah, kin san mijinki yana da karfin sha’awa, ba kya iya gamsar dashi, yana son ya kara aure kin hana, ki sani kina ingizashi zuwa ga afkawa fasadi da cin amanar aure ne
Ina ganin da ya miki kishiya ba ta hanyar aure ba a waje har yaje ya kwaso cutukan jima’i yazo ya zuba miki, ai gwanda ki barshi ya auro wata ya kawo gida ku zauna cikin aminci
Don haka a ji tsoron Allah a kara aure
Allah Ya taimakemu
SAIWAR ZOGALE
Da farko ina neman addu’a ga duk Wanda ya karanta ya karu,Allah ya biya mana bukatumu na alhairi.