HANYOYIN GAMSAR DA JUNA
Hanya ta farko da za ku fara bi wajen gamsar da mijinku shi ne nuna masa shauki da zumudin son yin jima’i, kada ku nuna jin kunya domin nuna masa zumudi wajen saduwa zai ba shi damar shirya kansa da kuma yin zumudi shi ma, wanda idan haka ta faru kun taka wani mataki na gamsar da shi domin kin motsa masa sha’awarsa.
Yayin jan hankalinsa ki yi kwalliya da ado, ki fesa turare mai sanya shauki, sannan ki rika yauki da shagwaba da kuma kisisina.
Hanyar jan hankalin miji ta hada da rausayar da jiki, sanya tufafin da za su fitar da sura don hakan ya kara janyo hankalin miji.
Murmushi, yin kalamai cikin tausasa murya, wani lokaci mai cike da sigar rada tana haifar da motsuwar sha’awar mazaje. Yin kalaman barkwanci, yin wasa ga miji da sauransu.
HANYA TA FARKO
A kullum ko lokaci-zuwa-lokaci ku rika amfani da sabbin hanyoyin yayin jima’i wajen gamsar da mijinku, kada a kullum ku rika amfani da salo daya yayin kwanciya hakan zai sa ku gunduri mijinku. Kada ku manta jima’i kamar cin abinci ne, mutum yakan so ya samu canjin abinci ko dandano, to haka batun jima’i yake, yana bukatar salo-salo don a samu dandano daban-daban. Amma sai ka ga wadansu matan sun kwanta kawai ba tare da yin wadansu dabarun da zai kara wa mijinsu karkashin son yin jima’i har ya samu gamsuwa ba.
HANYA TA BIYU
A lokacin da aka zo jima’i yana da kyau mata su karfafa wa mijinsu gwiwa, ba kamar wadansu matan da suke zama ko oho ba, ba ruwansu da karfafa wa mijinsu gwiwa ba, idan ya samu karfin gwiwar gamsar da ku, to shi ma zai samu gamsuwa domin ya samu yakinin cewa ya gamsar da ku.
HANYA TA UKU
Yin wasanni Ba wai sai lokutan da za a sadu ba, ya kama ku rika yi wa mijinku wasanni a wadansu lokutan da kuka lura yana cikin nishadi. Za ku iya masa wasannin ne ta hanyar shafarsa, sosa gashin kansa, tattaba yatsunsa da lankwasa su, inda wani lokaci za ku rika zungurarsa kadan. Yana da kyau ku rika ba shi labarai masu ban dariya da sanya nishadi, wani lokaci ku rika zolayarsa, yanayin yadda zai rika sake jikinsa gare ku zai nuna muku yana samun gamsuwa. Ta wannan hanyar ma za ku iya isar da sakon nuna son jima’i ba tare da bayyanawa da baki ba.
Duk Wata Mace Tana Son Mijinta Ya Rika Yi Mata Wadannan Abubuwan Idan Suna Kan Gado:
SHARE
#Tsangayarmalamtonga
Akwai wasu abubuwa da damar gaske na farantawa matarka rai da baka yi mata ko masu. Haka nan na faruwa ne kodai bakasansu ba ko kuma bakada damu daka mata ba.
Da akwai wasu abubuwa na musamman da mata suke bukatar mazansu suna musu idan suna kwance amma ba duk mace bace zata iya fitowa sarari ta sanar da mijinta tana so ba.
Ga wadannan abubuwan da duk wata mace zata so mijinta ya mata akan gado:
#darasi
1: Duk wata mace tana son tana kwance a jikin mijinta suna hira har lokacinda bacci zai kwashesu.
Amma sai ka tarar mace na kwance a daki miji na zaune a falo babu hira har bacci ya kwashesu.
Abokina yi kokari ka kwantanta kwanciya da matarka tana jikinka kana mata wasa da wani bangare na jikinta har sai kaji ta soma bacci idan kanada abunyi sai ka tashi kayi.
2: Kusan lokatai da dama muna yin magana akan yadda tausa yake da matukar tasiri wajen inganta soyayyan ma’aurata.
Mata da yawa suna son mazansu su rika musu tausa a lokacinda suke gado domin cire mata gajiyar data yini tana aiki.
Tasirin da kuma tausa yake dashi bayaga fitar mata da gajiya, kana iya motsa mata sha’awar ta koda kuwa a farko batada niya tsammaka.
Don haka mu daure muna yiwa matanmu tausa akai-akai saboda ba duk macece bace zata fito ta fadawa mijinta tana bukatar ya mata tausa ba.
Domin ita mace muddin ba mijinta ne zai mata ba, ko diyarta mace idan tanada ita kuma ta kai munzalin yi sai kuma kanwanta idan tana da ita.
Amma shi namiji a irin nasa iKon zai iya zuwa gidan tausa a masa ko namiji ko macece zata masa bazai damu ba, amma ita kuwa hakan bazai yiwu ba.
3: Wuya da goshi wurare ne na musamman da mata suke bukatan a sumbancesu a wajen. Hakan yasa mata suke son jin maigida ya sumbaceta musamman a goshinta a matsayin mu kwana lafiya.
Alhaji gwada yiwa matarka hakan a yau din nan gobe kaga irin yadda zata tashi da annashuwa.
4: Duk wata mace, zan kara maimaitawa, duk wata mace tana sone taji tana bacci a jikin mijinta a rungume da ita ko ita ta rungumeshi suna bacci.
Macen da mijinta ya saba mata da wannan kwanciyar yin bulaguro ya jima da banashi bane. Domin ta daina yin bacci mai dadi kenan har sai mijin ya dawo.
Maza sai mu kiyaye wannan bangaren da madam take so.
5: Mata suna son mazansu su ciyardasu wani cima na musamman a lokacinda ake kan gado kamin bacci.
Ta zauna ka saka mata inibi, tufa, kanka, alawa ko wani zuma kuma hira. Tana shagwaba ya isheta kana cewa sai kinci.
Sai dai kashi, ba duk maza suke yiwa matan nasu hakan ba. Suma matan ba duka bane suke iya bude baki sucewa mazansu suna so ba.
Kada ka dauka itace Jima’i kawai take so da zaran ta hau gado da mijinta. Irin wadannan abubuwan ga mata masu son ganin soyayyar mazansu, sunfi damuwa da irin wadannan abubuwan fiye da Jima’i.
Da fatan maza zamu daure mu dauki wasu daga cikin wadannan abubuwan domin farantawa matan mu rai.
Ka tuna fa, ita mace banda kai din nan babu wani namiji daban da zai iya ko halasta ya mata wadannan sai kai. Kai kuma Kila kanada wasu matan banda ita. Ko wata can da kake mata hakan ko lada babu.