Tirkashi: Mawaki Hamisu Breaker Yayi Martani Ga Batun Ramiya Moussa Nijer - Hadiza Gabon.
Idan me sauraro Yana bibiyar kafafen sada zumunta na social media a 'yan kwanakin Nan zaici Karo da wata Hira da akayi tsakanin Rakiya Musa da Kuma jaruma Hadiza Gabon, inda Gabon yayiwa Rakiya Musa tambaya akan tsohon saurayinta shin wacce kalar yaudara yayi mata.
Ai kuwa Nan take Rakiya Musa ta saka kuka Kuma ta nunawa duniya cewa hakika ya yaudareta Kuma bazata ta6a mantawa da hakan ba, yayin da take fada cikin kuka.
Kuma ta bayyana cewa hakan ya dakatar da ita akan kudirin da yake da ita nayin aure Koda zuwa gaba saboda bazai yuwu taje Gidan wani a matsayin matar aure ba Kuma Yana tunanin wani daban.
Sai a Safiyar wannan Rana Kuma Muka tashi da wani Bidiyo da Hamisu breaker ya wallafa a shafinsa na Instagram inda ya nuna tsarguwarsa karara a Kan wancen kalamai na safiya musa, inda shima ya mayar da Martani akan maganar ta ta duk da cewa ita Bata ambaci suna ba.
Idan Mai sauraro Yana bibiyar labaran kannywood zaiji wani lokacin inda aka Rinqa challenge din Hamisu breaker akan cewa duk wacce yayi bidiyon Waka da ita sai taji Tana son shi.
Shin menene Ra'ayin me sauraro akan hakan?
Mu hadu a comment section.