Abubuwan Da Ake Bukata:
a. Hulba
b. Gyada.
c. Alkama
d. Ridi
e. Shinkafa
f. Karas
Wadannan kayan abinci ake bukata mace ta tanada. Abin da za ta yi shine, ta samu garinsu. Abin nufi kamar shinkafa, sai ta gyara ta sosai ta daka ko nika yadda za ta samu garinta. Haka za ta yi wa gyada, ridi, da alkama. Ita kuwa hulba sai ta sayo garinta, shi kuma karas sai ta shanya shi ya bushe sannan ta samu garinsa.
Bayan ta sami garin wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraye, daga nan ta adana su a mazubi mai tsafta, kuma mai murfi.
Yadda za ta yi amfani da wannan hadin gyaran nono shine, za ta sami madara ‘Peak’ idan son samu ne, ta ke zuba wa ta sha a kullum. Za ta sha mamaki matukar ta juri amfani da wannan hadin gyaran nono, domin kuwa nononta zai dawo tamkar na budurwa, da iznin Allah.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan Bayanin game da wannan maganin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.