Yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan mar-mari
- Wake
- kifi
- Nama
- kwai da sauransu
- Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su
- Salat
- kabeji
- Alayyafo
- zogole
- Lemu
- kankana
- Apple dasauransu .
Wanda cin abinci lafiyayya yana karawa mata jini , lafiya , yana karawa yaron da yake cikib ta lafiya da kaifin basira .
Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane
mace mai juna biyu baikamata tadinga aikin wahala sosai ba , yakamata tadinga hutu ko wacce rana .
idan mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibity domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ,ko zai yakawo matsaka ga yaron cikinta .
tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .
maccen da take yawan amai yakamata tayi amfani da busheshshen abinchi wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .
Zuwa awu (Antenatal) yana da amfani sosai wanda alokocin awu za a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki .
Kuma ana auna aga wassu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su da wuri.