Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bayyana rashin jin dadinta ga shawarin da gwamnatin Oyo ta yi na sauya sunan babban masallacin da ke Iwo Road a Ibadan zuwa sunan gwamna Seyi Makinde. Kungiyar ta addinin Islama ta kuma bukaci da a gaggauta mayar da tsohon sunan masallacin ba tare da bata lokaci ba. MURIC ta bayyana wannan batu ne ta bakin Daraktanta, Ishaq Akintola, kamar yadda ya wallafa a shafin kungiyar.
Yadda lamarin ya fara a tun farko A wata Juma’a a watan Oktoban 2019, gwamna Makinde ya sanar da rushewa tare da sake gina babban masallacin Adogba a wani wuri. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Gwamnan ya ce, za a kammala aikin sake gina masallacin ne cikin watanni tara zuwa 11, kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, cocin da ke yankin shima za a rushe shi tare da yin sabo. Ya zuwa yanzu dai an sake gina masallacin a wani wurin shekaru kusan hudu bayan da gwamnan ya yi alkawari. Abubuwan da aka saka a cikin masallacin A cikin masallacin, akwai makarantar Islamiyya, cibiyar nazarin addini, dakin karatu, dakin taro da kuma katafaren filin ajiye ababen hawa. Ta haka ne aka maka sunan gwamnan, inda MURIC ta bayyana rashin dadinta da cewa, gwamnan na son amfani da damar ne don cimma manufar siyasa.