Akasarin wadanda wannan matsalar ke damu sun kasance cikin kashi 98% daga tarin mata, domin suna zaune ne a karkara inda babu abinci mai gina jiki ishashshe, sannan kuma akwai karancin ilimi na zamani.

Wannan da wasu tarin dalilai suka janyo mata ke kasa gyara nonon su domin saida ilimi ake yin komai, sabanin haka kuma ba wai gyara jiki ba hatta tafiyar da yadda rayuwa zata kasance a gaba. Idan kuwa haka ta faru to komai ya lalace tun daga farko har zuwa karshe.

Matsalar zubewa ko kuma yakushewar nono abu ne na musamman da yake addabar mata a wannan lokaci, duba da irin wadannan dalilai masu tarin yawa dangane da al’amarin da yake alaka rashin waye wa.

Shawara ta bangaren hukumomi da masu aikin sa kai ita ce tayi karanci, domin idan akwai masu wayar da kan mata (musamman matan aure ko zawarawa) ta fannin kula da lafiya da tsaftar jikin su da kuma muhallin da suke zaune, tabbas ba za’aje ga wannan lamarin da ake ciki ba.

Lamari irin wannan (na kulada tsaftar jiki) yana bukatar a fadada shi ta hanyoyi da dama saboda halin zamantakewar iyali. Wasu mazan suna son matan su su kasance sun fita na daban a cikin jinsin su na mata, na daga sura da diri da cikar suffa ta mata.

To idan dai burin ki shine ki gyara tsayuwa da cikowar nonon ki, sai kiyi wannan hadin wanda zai bawa sauran abokan ki mamaki, sannan ki zama abar koyi kuma mai kwarjini a wurin su.

A yau zamu kawo muku hanyar da zaku bi domin ganin kun dawo da martabar sa.

zaki nemi kayan hadi kamar haka.

(1) Hulba
(2) Waken soya
(3) Gyada

Ga Bayani dalla dalla kan yadda za’a haɗa;

Waɗannan kayan haɗi ana niƙasu ne suyi laushi sosai da sosai, sannan a sai haɗa su wuri guda.

Bayan haka kuma za’a rinka shan su tare da madarar gwangwani ta ruwa kamar Peak, ko kuma Olympic, kodai duk wadda ta samu.

InshaAllahu za’a samu kyakkyawan sakamako.

Previous Post Next Post