Yadda Ake Kara Karfin Azzakari A Saukake:

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu yan uwa barkan mu da wannan lokaci, kuma barkanmu da saduwa a wannan shafi na Mujalla me farin jini, muna fatan ku na cikin koshin lafiya.

 

A wannan makala za mu kawo muku nau’ikan maganin karfin Azzakari don me karatu ya zabi wanda ya fi masa sauki ya jarraba. Dukka magungunan da mu ka rubuta a wannan shafi an yi amfani da shi kuma an dace, don haka za ka iya saukar kowanne ka yi amfani da shi. ALLAH YA sa mu dace.

 

Karfin azzakari wani sanadari ne na gamsar da iyali. A wasu lokutan akan samu rigingimu tsakanin ma’aurata saboda yadda wasu mazan ba sa iya biya wa matansu bukatar auren, har hakan kan kai ga rabuwa.

 

Mujalla ta bata lokaci mai yawa wajen bibiyar zanarce-nazarce ma su tarin yawa kan wannan mas’ala, sai mu ka yanke shawarar sanar da ‘yan uwa yadda za su kara karfin azzakarinsu don samun dankon zamantakewar aure, ba don komai ba, sai don mun yi amanna da abin da Hausawa ke cewa, “Idan ka na da kyau ka kara da wanka”. Sakamakon haka mu ka yi wa wannan makala taken “Yadda ake kara karfin azzakari a saukake”.

 

1.Dabino; Shi wannan hadin maganin kaefin maza Dabino kawai ake bukata.

 

Yadda ake amfani da shi, shine, ka samu dabinonka mai kyau guda 13 ko 15 sai ka wanke, ka zuba a mazubi mai tsafta sai ka zuba ruwa ya sha kansa, ka bar shi tsawon awa uku sannan ka cinye. Idan da hali ayi safe da yamma, amma idan ba hali sai aci da yamma kadai.

 Sai dai ba a son aci wannan hadi da zarar an kammala cin abinci, idan son samu ne ana son aci lokacin da ake jin yunwa, sai a jira mintuna 20 zuwa 30 kafin aci wani abinci.

 

2. Ga Kayan hadin wannan maganin karfin Azzakari:

 

a, Busassgen Ganyen Zogale da ‘ya’yansa b. Busasshiyar Citta c. Busasshen Kaninfari d. Busasshen Masoro sai kuma e. Busasshiyar Kimba.

 

Sai ka hade su ka dake su suyi laushi. Idan za ka wannan hadi, za ka debi karamin chokali ka zuba a shayi ba madara, bayan tsawon minti 15 sannan ka sha. Haka za ka ke sha safe da yamma.

 

Baya ga karin karfin azzakari, wannan hadin magani na maganin, sanyin mara ciwon da amosanin mara. Don haka maza da mata za su iya yin amfani da wannan magani.

 

3, Kayan Hadi: Muruci da Kanumfari da kuma Citta.

 

Ga yadda za ayi. Za ka samu Muruci danye, sai ka shanya shi ya bushe. Sai ka samu busasshen kanumfari da citta ka hada su waje guda ka dake.

Yadda Ake amfani da shi: Kullum za ka dinga zubawa a shayi ba madara kana sha.

 

4. Kayan hadin wannan maganin karfin maza da ake bukata.

Albasa da Tafarnuwa da Zuma da Citta da kuma Kanumfari.

 

Yadda Zaku Hada Maganin Cikin Sauki. Zaka dauki Albasarka mai kyau saika nika ta ko ka kirba sosai ta zama ruwa. Sannan ka dandaka ko kirba tafarnuwarka, sai ka daka Cittakar da Kanumfarinka su yi kaushi sosai .

 

Bayan ka kammala wannan aiki kamar yadda mu ka ambata a sama, sai ka samo kofi da cokali ka debi kamar cokali biyu na ruwanAlbasa, cokali biyu na ruwan Tafarnuwa, cokali biyu na garin Kanunfari da kuma cokali biyu na garin Citta. Tun da farko ka tanadi zumarka me kyau marar algus, sai ka debi cokali Hudu na Zuma ka hadasu a mazubi guda ka cakuda su sosai, sai ka shanye.

 

Za ka sha wannan gadin maganin karfin azzakari sau biyu a kowacce rana wato safe da yamma, insha Allahu za ka samu kyakyawon sakamako.

 

5.Ga wani hadin maganin kara karfin maza me saukin hadawa, kuma sha yanzu magani yanzu da iznin ALLAH. Ka sayi gaban dan Maraqi ko dan Akuya wanda ba a yi wa fid’iya ba, a dafa maka da kayan kanshi sannan sao ayi maka miyar kuka da shi ka dinga ci.

 

6. Shi ma wannan hadin ya na saukin hadawa. Ga abubuwan da ake bukata. Za a samu kwan kaza guda 2, babban cokali 1 na garin habbatus sauda, sai a cakuda su sosai, sannan a soya sama-sama kar ya kone, sannan a cinye.

7. KANKANA ; Kankana na kunshe da wasu sinadarai dake aiki kwatankwacin maganin karfin maza na zamani da ake kira ‘Viagra’ a turance. Don haka tana kara karfin maza sosai.

 

Don a samu amfaninta sosai za a sha mintuna 30 kafin fara jima’i. Ana bukatar a cinye har wannan farar tsokar da kuma ‘ya’yan. kuma kar a sha lokacin da ake koshe ko da zarar an kammala cin abinci, amfi son a sha kafin cin abinci kuma a saurara bayan an sha zuwa mintuna 20 zuwa 30 kafin a bi ta da abinci.

 

8. Ga kayan hadin da ake bukata kamar haka: Kanumfari da Citta da kuma Sanya. Duk wadannan kayan hadi za ka daka su ne don ka samu garinsu.

 

Bayan ka daka su, sai ka debi, Garin sanya cokali biyar, Garin Kaninfari cokali bakwai, da Garin Citta cokali daya. Sai ka hade su waje daya a mazubi me tsafta kuma me murfi, sai ka ke zuba karamin chokali a ruwan shayi ba madara ka ke sha duk lokacin da ka ke bukatar karfi da kuzari. Cikin kankanin lokaci yake fara aiki da iznin Ubangiji,amma an fi son ka ci abinci ka koshi kafin ka sha wannan maganin karfin mazan saboda yana da karfi.

 

9. Ga wani hadin maganin karfin azzakari me sauki kwarai da gaske. Ko a yanzu bayan karanta wannan makala za ka iya fara jarrabawa, kuma ina yi wa me karatu albishir cewa an gwada wannan maganin karfin maza kuma ya na aiki sosai, insha ALLAHU. Ka samu man Kanunfari ka shafa a gabanka mintuna 30 kafin kusantar iyali, za ka ji canji kwarai da gaske, kuma baya ga karin karfi ya na zanya a jima kafin a yi inzali.

 

Kuma kari a kan hakan sai ka samu Man Kanunfari da Man Zaitun ka hada su a mazubi guda ka dinga shan cokali daya kullum.

 

10. Shi kuma wannan hadin maganin karfin maza, ana bukatar, Habbatussauda da Zaitun da tafarnuwa da Zuma. Za ka daka Habbatussauda ko ka sayo garinta don samun sauki, shi ma zaitun garin ake bukata, haka ma tafarnuwa.

 

Idan kammala su, sai ka debi garin Habbatussauda karamin kofi daya, garin Zaitun shi ma karamin kofi daya, garin Tafarnuwa rabin kofi sai Zuma kofi biyu. Ka hada su waje daya ka cakuda su da kyau.

 

Yadda ake amfani da wannan magani shine, za ka dinga zuba cokali daya a shayi ba madara ka ke sha kullum sau daya, bayan ka ci abinci.

 

11.Namijin Goro; Cin namijin goro akalla guda biyu a rana ya kan dawowa namiji kuzarinsa. An jarraba an tabbatar da hakan sakamakon wasu sanadarai dake cikinsa mai matukar fa’ida wajen samar da karsashi ga maza.

12. Kayan hadin da ake bukata sun hada da. Alkama da Habbatussauda. Kowannen si ana bukatar garinsu ne.

 

A bukatar Alkama gwangwani hudu, a gyara ta da kyau sannan a nika ta don a sami garinta. Sannan sai a samu garin Habbatussauda kofi daya, a hade su waje guda a mazubi me tsafta. Kullum a debi cokali daya a zuba a rabin kofin shayi ba madara a ke sha.

 

 

13. ka dimanci shan zuma cokali biyu a cikin ruwan dumi kullum.

.

14. A samu saiwar Burqu da itacen Zumbur sai a hada su waje daya, kullum mai gida ya dinga sha sau biyu.

.

15. A samu danyen kwai kamar guda talatin. Kullum sai a dafa guda daya, sai ka cire kwanduwar, farin kwan kawai za ka ci tare da yankakkiyar albasa.

Kullum ka ci daya har kwan ya kare.

.

16. A samu gaban Ayu, sai a saka a cikin zuma har tsawon kwana bakwai. Idan ya juku sai ka dinga lasar zumar har ka shanye.

.

17. A samu Gurji da Ayaba, sai a markada ayi lemon juice a sa zuma mai gida ya dinga sha.

.

18. A samu busasshen Muruci da garin Kashe-Zaqi da Farin-Magani da Farin -Mauro. Sai a hada su waje daya a daka a tankade. Sai ka dinga zuba cokali daya a shayi ba madara kana sha kullum sau daya.

.

19. Ku samu Man Zaitun mai kyau, sai ka dinga shan cokali daya kullum kafin ka ci abinci.

 

20.Ka dimanci cin Dafaffen Muruci.

 

21. Ayaba; Ta na da sanadarai dake karawa namiji kuzari, sai a ci guda uku ko biyu kafin jima’i da mintuna 30. Kamar kankana ba a son cin ta da zarar an kammala cin abinci.

 

ZAKA IYA BADA SADAKA IDAN KAJI DADI MAGANIN:

 

LADUBBAN DAREN FARKO GA MA’AURATA

 

MATASA DA YAN MATAN WANNAN ZAMANIN SAI MU GYARA GASKIYA

 

Da ango ya shigo dakin sabuwar amaryarsa, bayan ya zauna, sai ya yi mata sallama cikakkiya, watau: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh,’

 

Ita ma sai ta amsa da irin haka, watau: ‘wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wabarakatuh.’

 

Ya fi kyau ya hada da mika mata hannu su yi musabaha tare da sallamar.

 

Sannan sai ya aza hannunsa na dama bisa saman goshin amaryarsa ya karanta wannan addu’ar:

 

‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’

 

Ita ma Amarya sai ta dora hannunta saman goshin angonta ta karanta kamar haka:

‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’

 

To daga nan sai su yo alwalla su yi sallar nafila raka’a biyu tare (watau cikin jam’i, ba daban-daban ba),

 

In sun idar sai su yi kyawawan addu’o’in duk da ya kamata, su roki Allah Ya sa alheri cikin rayuwar aurensu; Ya ba su zuriya dayyaba; ya ba su tsananin hakurin zama da juna, ya sa su kasance tare har Aljanna, da sauran bukatocin da suke fatan samu cikin rayuwar aurensu.

 

To bayan nan, ana so su dan tattauna tsakaninsu, kuma tattaunawa ta gaskiya tsagwaro ba tare da wani boye-boye

ba, tun da dai an riga an zama daya.

 

Ango ya gaya wa amaryarsa dukkan irin abin da yake so da wadanda ba ya so,misali ya ce: ‘Kin ga dai ni mutum ne da ba ya son raini, don haka ki yi kokarin kiyaye dokokina matukar ba su saba wa dokar addininmu ba, sannan kuma ba na son yawan fita ba tare da kwakkwaran dalili ba.

 

A fannin abinci ni mai son tuwo miyar kuka ne, ina kuma son fura da nono kindirmo,’ da dai sauran bayanai makamantan wadannan.

 

Haka ita ma amarya sai ta bayyana wa angonta dukkan abin da take so da wadanda ba ta so, kuma su duka su yi niyya mai karfi ta kiyaye hakkin juna, don samun zamantakewa mai kyau, mai dadi, wacce za ta iya fuskantar kowane yanayi na rayuwa ba tare da ginshikinta ya girgiza ba ballantana har ya tuge.

Daga nan sai su karanta wani littafi na addini da ya yi magana a kan fikihun aure, don su kara sanin hakkoki da irin nauyin da ya rataya a wuyan kowanensu. Ko kuma su samu wani faifai na wa’azin malamai a kan aure, su kalla ko ji tare suna masu tattauna abubuwan karuwa da suka ji a ciki.

 

Daga nan sai a yi shirin kwanciya barci. Yana da kyau sababbin ma’aurata su san cewa, ba lallai ba ne sai sun gabatar da ibadar aure a ranar.

 

Suna iya yin ’yan wasanni kadan-kadan na nuna so da kauna, kuma inda za su maimaita hakan akalla sau 7, ya zamar masu kamar wani dan kwas ne na fahimtar yanayin sha’awar juna, da kuma gane yanayin jikin juna da kuma gano malatsar sha’awar juna; in har za su iya wannan jinkirin, zai kara dandano, zimma da lazzar kayatarwar cikin ibadarsu; haka kuma sai ta kara samun cika da fa’ida; domin in aka yi haka da wuya a samu matsala.

 

In ma an lura da matsala ana iya magance ta a wannan lokacin jinkirin.

 

Lokacin gabatarwar ibadar aure, ango sai ya daure ya bi a hankali da amaryarsa, domin zuciyar kowace sabuwar amarya cike take da tsoro da fargabar abin da ke shirin faruwa da ita,

 

kuma akwai yiwuwar ta ji tsananin zafi, don haka in ango ya bi ta a hankali, zai iya rage mata wannan zafin da rudin da take ciki.

 

Kasawar sabon ango ran daren farko ba abin fargaba ba ne,don shi ma yana cikin fargaba da tsananin dokin yin wani abu a karo na farko wanda wannan na iya zauzautar da abubuwa gare shi, don haka sai ma’aurata su sa hakuri su kara gwadawa, su yi ta gwadawa har sai ango ya lakanci abin sosai ya iya rike kansa har sai lokaci mafi dacewa.

 

Kuma kada amarya ta yi wa angonta dariya dalilin wannan; ko ta ce dama bai isa auren ba aka yi masa, ko ta ji haushin sa, sai dai ta kasance masoyiya kuma uwargida ta kwarai wacce ke tallafawa mijinta a kowane lokaci.

 

Ango, sai ya yi hakuri da rashin tabuka komai daga amaryarsa, kada ya ji haushin ta ko ya fara tunanin bai auri irin matar da yake so ba; mata suna da tsananin kunya ta bangaren bayyana jin lazzar sha’awarsu, abin har ga matan da suka dade da aure, balle kuma sabuwar amarya?

 

Amma in ya yi niyya, kuma in har yana so, cikin dubaru da fasaha da yawan yabo, a hankali sai ya bice kunyar nan daga gare ta har ta rika yin irin yadda yake so.

 

Amarya kuma ta sani: in ta daure, ta kanne, ta cije, ta fara cire kunya tun ran daren farko ya fi alheri a gare ta da dorewar farin ciki a rayuwar aurenta.

 

Kafin gabatarwar ibadar aure, yana da kyau ga sababbin ma’aurata su san dukkan ladubban ibadar aure; kuma su tanadi dukkan abin da ya kamata su tanada.

Previous Post Next Post