☛ MAZA AJI TSORON ALLAH DAGA CIKIN ABINDA YAKE JEFA WADANNAN MATAN WANNAN HARKA ITACE ( RASHIN GAMSAR DA JUNA ( JIMA’I ) KO WANI BAYA DA LOKACIN MATAR GABA DAYA*
_wanna yasa Mata da yawansu shaye-shaye da madigo_
*☛ SAI TAYI KARATU – TAYI KARATUN AMMA TA DAWO DA CIKI KO TA ZAMA YAR MADIGO HABA ALHAJI WANNA RIBA CE KA SAMU KO ASARA A RAYUWAR KA.
• shawara itace Inda har yaran Ku mace KO namiji sun nuna.
suna da bukatar aure yana da kyau kayi kokarin haka domin Sha’awa bata da Garkuwa jikin Dan adam :
*SAI A KIYAYE DOMIN WADANNAN MATSALOLIN MU DA KANMU MUKE JIFA SU CIKIN AL’UMMA*
Madigo, kamar sauran abubuwan da suka gabata ne (yana da illa) wajen haifar da cututtuka da bala’i da musiba ga mai yin sa. Ga kadan daga cikinsu:
1. Madigo fita ne daga dabi’ar da Allah Ya halicci mace a kanta, ta jin dadi da da namiji ba mace ’yar uwarta ba.
2. Cikin Madigo akwai rashin kunya da fitsara, alhali Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Kunya alheri ce gaba dayanta.” A wata riwaya: “Kunya ba ta kawo komai sai alheri.” Buhari ne ya rawaito.
3. Madigo yakan haifar da cutukan zamani. A wani bincike da aka gabatar, ya tabbatar da za iya daukar cutar kanjamau ta hanyar madigo, idan aka yi da wadda take dauke da ita, kamar yadda za a iya samun ciki ta hanyar madigo, idan mace ta yi da wadda ba ta dade da saduwa da da namiji ba. Haka nan likitoci sun tabbatar da madigo yana iya jawo rashin haihuwa.
4. Ana iya rasa budurci ta hanyar madigo, wanda hakan ba karamin tozarta ba ne ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure.
5. Mai madigo takan rayu cikin kuncin zuciya da kunarta, saboda Allah zai debe mata natsuwa a tare da ita, Ya maye gurbinta da kunci da damuwa. Wata budurwa ’yar shekara ashirin tana ba da labarin irin yadda ta samu kanta cikin damuwa da bala’i bayan rabuwarta da abokiyar madigonta.
Tana cewa: “Na kasance budurwa ’yar shekara ashirin, ina son wata kawata sosai tsawon wasu shekaru masu yawa, har dai muka fara madigo a tsakaninmu, ta shiga raina matuka, na zama duk abin da take so shi nake yi, har ma ya zamana wani lokaci ana samun sabani tsakanina da ita idan na ga wani ko wata suna kaunarta, saboda yadda nake kishinta. Wata rana sai wannan kawar tawa ta yi aure, abubuwa suka canza, ta ce dole ne mu rabu. Haka muka rabu, ni kuma na shiga wani hali na jin zafi da radadi a jikina da zuciyata! Ciwon kai, ciwon idanu, ciwon jiki, na je wajen likitoci amma ban samu wata waraka ba, wayyo! Ni yanzu yaya zan yi, ga shi na tuba, amma fa ina so in koma wajenta, yaya zan yi!? Wannan kadan ke nan daga illar madigo.
6. Madigo yakan hana ’ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, to zai yi wahala ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta rika fita tana yi, har idan Allah Ya tona asirinta, mijinta ya sake ta, saki na wulakanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da madigonta, don haka: “Maganin yaya za a yi, (shi ne) kada a fara.”
7. Mai madigo ba ta karewa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haduwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai kabari!
8. Madigo dabbanci ne! Kai! Dabba ma ta fi ’yar madigo.
9. Cikin madigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da Ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji.
10. Haduwa da azabar Allah a Lahira, idan ba a tuba ba.
Wannan kadan ke nan daga cikin illolin da madigo yake haifar wa masu yin sa. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu.
Hanyoyin kare kai daga zina da luwadi da madigo:
Saboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya auka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun samu inda za su zubar da sha’awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa aukawa cikin zina:
1. Aure: Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: “To ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba.” (Annisa’i: 3).
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma yana cewa, “Ya ku taron samari! Duk wanda ya samu iko (ma’ana zai iya rike mace) to ya yi aure, domin shi ne mafi abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sa a tsare farji. Duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi, domin (shi azumi) kariya ne a gare shi.” Buhari da Muslim.
Wannan aya da Hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matukar ba ta cikin wadanda Allah Ya haramta masa ya aura. Saboda haka da mazinata da ’yan luwadi da masu madigo za su yi tunani da sun ga yadda Musulunci ya sauwake musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zama duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah Ya ba su lada, kamar yadda Hadisi ya nuna.
FYAƊE A MAHANGAR MU DA MAHANGAR SU.
MAL.AMINU IBRAHIM DAURAWA:
Musulunci ya haramta zina da madigo da luwaɗi da bin dabba da amfani da hannu, da amfani sashin jiki wajan biyan buƙata, ko amfani da azzakarin roba, ko yarbebi ta jima’i, ya hana auran jinsi mace da mace namiji da namiji, ya hana auran dabba da mutum kamar namiji ya auri karya ko mace ta auri kare, ya hana ɗaukar amarya,. wato fyaɗe,
Ya haramta duk wata hanya ta biyan bukatar sha’awa idan ba aure ba.
FYAƊE
Abinda ake kira Fyaɗe shine yin amfani da ƙarfi, ko wata barazana, wajan tilasta wani ko wata wajan yin lalata, kamar namiji ya yi wa mace Fyaɗe ko mace ta yiwa namiji Fyaɗe, ko namiji ya yiwa namiji Fyaɗe ko mace ta yiwa mace Fyaɗe, ana yi wa yara Fyaɗe ana yi wa manya Fyaɗe, ana yi wa maza ana yiwa mata, amma a wajan turawa Fyaɗe ya haɗa da auran ƙananan yara da duk wani Shekaru da doka ba ta amince ba ayi aure, ko zina ko luwaɗi ba tare da cikar wannan shekaru ba shima yana cikin Fyaɗe, amma idan shekaru sun cika, kuma anyi da yarda da amincewar ɓangaran guda biyu, to wannan zina ko luwaɗi ko auran jinsi a wajan su ba laifi bane, wannan shine banbanci tsakanin fyaɗe a wajan turawa da mu, su sun hallata zina da liwadi da madigo da auran jinsi da auran mutum da dabba, mu kuwa wannan duka haram ne,
Don haka Fyaɗe shine yin zina da ƙarfi ko yin luwaɗi da ƙarfi ko yin maɗiko da ƙarfi, (suna saka auran wuri a cikin fyaɗe amma mu a wajan mu ko da wata kasa ta musulmi ta yanke shekarun aure ba za a ɗauki wanda ya yi auren wuri a matsayin wanda ya yi fyaɗe ba) idan aka yi waɗannan bisa yardar dukkan ɓangaran da amincewar su, wannan ba a kiran sa Fyaɗe, a wajan su. duk da ƙananan yara ba a yin lalata da su ko sun amince saboda ba su mallaki hankalin su ba, kuma ba susan abu mai cutarwa ko mai amfani ba. don haka yin amfani da ƙananan yara da basu mallaki hankalin su ba, laifi ta ko wacce hanya.
Abubuwan da zaa duba akan matsalar fyaɗe shine. Wasu matakai guda goma
1, kafa wani kwamiti mai ƙarfi wanda zai shafi dukkan masana, domin yin nazari akan yadda Fyaɗe yake faruwa
2. Shirya faɗakarwa akan yadda iyaye zasu sa ido akan ƴaƴansu, da kuma yadda zasu tsaya wajan neman haƙƙin su.
3. Wayar da kan al’umma akan illar yin fyaɗe, a dukkan mahaɗa ta al’umma.
4. Tilastawa asibitoci karɓar ces ɗin fyaɗe cikin gaggawa a ko wanne lokaci, domin idan babu rahotan likita ana shan wahala a kotu wajan tabbatar da faruwar abin har a ƙarshe wanda ake tuhuma ya kuɓuta.
5. Sanar da yan sanda ko ta kwana gamai da fyaɗe, domin tattara sheda kafin ta lalace, domin sai kaji a katu ance wane irin kaya ne a jikin sa.
6. Samawa iyaye lauya mara kwaɗayi, domin idan wanda ya yi fyaɗen mai gata ne, kuma waɗanda aka yiwa ƴarsu marasa ƙarfi ne sai a juya abin a kotu.
7. Samar da alƙalai masu tsoran Allah waɗanda zasu dinga duba maganar Fyaɗe bisa adalci da gaskiya, akan wanda ake zargi da wanda aka yiwa.
8. Cirewa mutane al’adar rashin bin haƙƙi, da kuma tsoran abinda zai sami yarinya bayan ta girma idan ƙarama ce, ko surutun jama’a idan babbace, cewa ba su da laifi a shari’a.
9. Kada a koma gefe a bawa iyaye kuɗi su janye tuhuma, idan wasu suna amfani da ƴaƴan talakawa, idan anje kotu sunga alamar zaa yi nasara sai su bawa iyayan maƙudan kuɗi sai su janye, wannan ma yana faruwa
10. Idan an tabbatar da laifi akan mutum babu wata shubuha ayi gaggawar yi masa hukunci, ba tare da ɓata lokaci ba.
11. Kuma a Samar da hukunci na bai ɗaya wanda zai zama ya tsawatar, babu sani babu sabo.
12. A Samar da kwararrun lokitoci da za su dinga duba lafiya waɗanda aka yiwa fyaɗe, da yi musu aiki domin ceto raunin da aka yi musu kuma kyauta.
HUKUNCIN FYAƊE A MUSULUNCI.
Malamai sunyi bayani akan yadda za a hukunta, mazinaci wanda shine irin hukuncin da ake yiwa mai fyaɗe, mai aure a jefe shi, mara aure ayi masa bulala ɗari kuma ayi masa ɗaurin shekara, ita kuma sai a duba yadda ya lalata ta, sai a ɗaura masa biyan kuɗi wanda zai zama tara ga abinda ya yi mata, wasu malamai sun kira shi sadakin auran ta, wasu kuma sun kira shi tara. idan kuma ya yi amfani da makami, sai a fassara shi a wajen wasu malaman da hiraba wato fashi, sai a kashe shi yadda ake kashe yan fashi da makami. Kamar ɓarawo ne da ɗan fashi duk sata sakayi amma shi ɗan fashi ya yi amfani da makami, wannan shine ra’ayin wasu malamai, waɗanda suke ganin zaa yiwa mai fyaɗe hukunci biyu idan yayi amfani da makami kamar yadda ƴan fashi suke yi suje gidan mutum suyi sata sannan su afkawa iyalan sa.
ALLAH SHINE MAFI SANI.