Daga zarar ciki ya shiga mace za tasamu wassu alamomi da bata saba ji ba, (ma’ana alamomin juna biyu kenan) daga cikin alamomin akoi.

(1) Ketaren wata.

(2) Tashin zuciya.

(3) Gajiya.

(4) Amai.

(5) Nonuwa suna kara girma.

(6) Zazzabin safe.

(7) Yawan fitsari.

(8) Yawan kwadayi.

(9) Karuwar karfin sha’awa.

Wadannan alamomin baza su tabbatar da cewa mace tana dauke da juna biyu ba, a dai-dai wannan lokocin mace ya kamata tayi gwajin fitsari ko jini domin tabbatar da cikin.

An raba ciki zuwa zango uku:

(1) Zango na farko yana farawa daga shigan ciki zuwa watanni uku.

(2) Zango nabiyu yana farawa daga watanni uku zuwa wata shidda.

(3) Zango na uku yana farawa daga watanni shidda zuwa haihuwa.

Hanyoyin da mace mai ciki zatabi domin zama cikin koshin lafiya:

Idan mace tayi ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta sabida shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini.

Ya kamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu da kuma kayan marmari:

(1) Wake.

(2) kifi.

(3) Nama.

(4) kwai da sauransu.

Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su.

(1) Salat.

(2) kabeji.

(3) Alayyafu.

(4) zogole.

(5) kankana.

(6) Apple dasauransu.

Wanda cin abinci lafiyayya yana karawa mata jini da lafiya yana karawa yaron da yake cikin ta lafiya da kaifin basira.

(2) Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane.

Mace mai juna biyu bai kamata tadinga aikin wahala sosai ba, yakamata tadinga hutu ko wacce rana.

Idan mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibity domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ko zai kawo matsala ga yaron cikinta.

Tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka.

Macen da take yawan amai ya kamata tayi amfani da busheshshen abinci wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya.

Zuwa awu yana da amfani sosai wanda a lokacin awu za’a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki da, kuma girmansa da kwanakin cikin.

Kuma ana auna aga wasu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su kamar su:

(1) Hawan jini.

(2) Ciwon sugar na masu juna.

(3) Cutar kanjamau.

(4) Yawan Jini.

(5) Zazzabin cizon saura.

(6) Alamar Eclampsia.

(7) Ina gargadin mata da su dinga amfani da maganin karin jini da ake basu a wajen awu.

Mafi yawan mata idan anbasu maganin karin jini mai makon suyi amfani dashi kullum amma basa amfani da shi, da sunan basa son warin maganin wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zaisa a hana mutum shan wannan maganin.

(5) Sai Kuma daukan allurar tetanus, wannan wata allurace da akeyiwa mata lokacin awun ciki amma mafi yawa mata basa son wannan allurar sabida rashin sanin amfaninta.

Gaskiya wannan allurar tana da amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shine kare yaro daga kamuwa da wannan cutar mai hatsarin gaske wato “Tetanus”.

(6) Motsa jiki lokacin juna biyu nada amfani sosai ga kadan daga ciki.

Yana taimako wajen rage ciwon baya, tashin zuciya, kumburin kafa da kuma kunburin Jiki.

Yana taimako wajen kare ko lura da ciwon suga na lokacin goyon ciki.

Previous Post Next Post