Rashin Lafiyar Fatima Wacce Aka Cirewa Kafa Ali Nuhu Yabawa Iyayen Kyautar Naira Miliyan 2
Jarumi Abdul Sashir wanda aka fi sani da malam ali na cikin shirin dadin kwana casa’in 90 mai dogon zango, ya bada labarin yadda wani abokin sa ya yabi Sarki Ali Nuhu wajen aikata alheri, yadda Ali Nuhu ya dauki kudin aikin sa kacokan ya bawa wata yarinya mai talla datayi barin awarar ta, Tun daga lokacin abokin nasa yace yake jinjinawa Ali Nuhu ga yake masa kallon mutumin kirki ne.
Ga wallafa da Abdul Sashir ya yi akan mutumin da yabi Ali Nuhu.
Nan take yaje har inda yarinyar take yatsaya yake tambayarta shin mene yake faruwa dake? Saitace awaratace ta bare sai yace to daina kuka kinji ya dauki kudi masu kauri yace ga wannan rike nabaki duka kije Ammafa kidaina kuka.
Bayan Ali Nuhu yashiga mota yatafi sai mutanan wajan sukace wannan kudinda Daya bawa wannan yarinyar fa yanzu yayi aikin wani voice over aka bashi kudin, ko Aljihu Bai saka kudinba ya dauka yabawa wannan yarinyar.
Abokina yace shifa tundaga Nan ya sallamawa Ali Nuhu akan gaskiya Wannan mutumin kirkine.
Jiya nake Hira da wani abokina sai yake cemin Abdul walh Ali Nuhu yatabayin wani Abu Wanda yatabani,nake tambayarshi mene yafaru? Sai yace watarana yaga wata yarinya Mai tallan awara tana kuka alamar tayi barin awararta. Saiga Ali Nuhu yafito Yana zuwa yaga yarinyar tanata sharbar kuka.
Talla babban illace ga rayuwan yaa mace ko da kuwa karaman yarinya ce.
Kaman yanda natakaita managar a shafina nace talla ya zama bara zana ga ƴaran mata yanzu, musanman masu sayar da abinci, gyaɗan, pure water, masa, kwankwa mati, ƙwai, kuli kuli, dama rauran su.
Wasu iyayen suna sakawa ƴaran mata talla ne saboda su nima abin da za su ci kuma su kara rufa ma Kan su asiri saboda babu yanda za suyi, amma ana samu wasu iyayen suna sakawa ƴaran su talla ne saboda son abin duniya alhalin Allah ya rufa masu asiri babu shakka wannan babban kuskuri ne ga iyaye mata
Watarana kusan sau uku ina ganin ana zubar da “masa” a bayan gidan mu abin ya sha bani mamaki ina “tambayan” kai na shin wa yake wannan aikin? ya zubar da “masa” masu kyau alhalin bai lalace ba, sai wani lokaci nafito daga gida misalin karfe goma na safe sai nayi ido biyu da mai wannan aikin ashe wata ƴar talla ce idan aka bata talla sai ta zubar da shi, kuma ba karaman yarinya ce ba budurwa ce take wannan aikin. sai na “tambaye ta” ko me dalili idan aka baki talla kina zubar da shi? sai tace ai wani Alhaji ne yana mani juye kullu idan nafito wurin sa nake zuwa sai ya min juye kuma yakara bar mani “masan” shi yasa nake zubar da shi domin kuwa idan bai kare ba mamana sai tayi mani kukan tsiya, sai abin ya bani mamaki da tace wani Alhaji ne yana yi mata juye kullu
Da yawa iyaye mata suna kuskure ki baiwa yarinya talla kice kar ki yarda ki dawo da wani abu agidan nan sai ya kare wannan kuskuri ne babban saboda wannan kalma yana iya sa yarinya ta fa ɗi daga sherrin zina saboda tana tsoron kar ta dawo da wani abu, tana iya bayar da kan ta domin ta samu kuɗin da zata baiwa wace ta bata talla gudun kar ta sha dukan tsiya.
Wani lokaci ina tunani ko ƴara da ake basu talla kaman ba iyayen su ba ne, ƴaƴan goyo ne, domin nata ƴaƴan suna makaranta suna karatu sabado ba za ta yarda nata ƴaƴan suyi talla ba amma ita za ta baiwa ƴaƴan wasu talla. yana da kyau kusawa ƴaƴan ku ido agidan goyo
Kuma kaman yanda na faɗa a baya talla illace ga yaa mace a wurin talla ce idon yarinya yake buɗe saboda tana hurda da maza iri iri kuma a wajen ne ƴan isaka suke zama ka gani lalacewa mai sauki ne, kuwa a wajen ƴan iska ko da kuwa kina da tarbiya sun san yanda za suyi su ɓata maki rayuwa Allah ya kyauta.
Sau da yawa ƴara da a kafi masu fyde ƴan talla ne mafi akasarin cikin su ƴan talla ne, Allah ya kyauta
Yana da kyau amasayin ka na uba kasa idanuwa ƙwarai da gaske akan ƴaƴan ka, ganin ka basu tarbiya da ilimi kuma har in dai kafi karfin abin da za ka ci kar ka yarda ka bari ƴaƴan ka suna talla ko da kuwa suna gidan iyayen ka ne,
Yaa Allah ka worewa kowa yafi karfin abin da zai ci na yau da kullun.
Abdullahi Waziri
Babban abu takaici shi ne matan aure masu yin tiktok kifito kina nuna ma duniya suranki.
A tunani na ƴan mata ne ƙawai suna yin Tiktok ashe har da matan aure suna yin Tiktok, babban abun takaici ne matar aure tafito Tiktok tana nuna suranta a Tiktok shi ne waye wa.
Na so in yi wannan maganar tun ba yau ba amma Allah bai bani iko ba sai yau
Babban kuskure ne kasan matar ka tana yin Tiktot kuma ka bar ta tana yi tabbas aƙwai gudomawan wasu mazajen wurin lalacewar zuri’ar su, sau da dama za ka gani mata da miji suna rawan batsa a Tiktok, rawan rashin kunya da rashin tarbiya da rashin sanin addinin musulunci.
Tabbas aƙwai wa yanda ba su san matan su suna yin Tiktok ba, shi yasa matan suna yin abin da su ka ga dama a social media kuma duk matar aure da take yin haka tabbas ta ci amanar mijin ta kuma ta ci amanar aure domin Allah kaɗai yasan abin da take aika ta a social media, Allah ya kyauta.
Wani abun takaici da ka ga yarinya yar shekaru 18 izuwa 20 tana yin Tiktok kuma tana nuna suranta a Tiktok kuma duk maganar da yafito daga bakin ta zata yi na rashin kunya da rashin girmama na ga ba da su, kuma da yawa ƴan matan Tiktok tallan kan su suke yi dama can ƴan iskane
Kuma kin gama nuna ma duniya jikin ki da tsarai cin ki da rawan iskanci ki ce miji kike nima saboda baki da kunya ko kin dauki kowa irin ki ne, ai sai dai ki aure ɗan Tiktok irin ke, Allah ya kyauta
Magana na ba ina nufin ko wace mace mai yin Tiktok ne halin su ɗaya ba ina nufin wasu daga cikin su ne, ba duk kan su ne ba Allah ya kyauta.
ƴan mata masu yin Tiktok kuji tsoron Allah ku tuna za ku mutu ku koma ga Allah ku dai na abin da kuke yi a Tiktok
Yaa Allah ka kara shiryar da ƴaƴan mu ƴan uwan mu kan nin mu da rauran al’ummah baki ɗaya, Allah kasa mu dace.