Don magance wannan matsalan zaki bi hanyoyi kamar haka:
*Wanke gaba da gayen magarya ko miski ko kanunfari ko alim ko kuma bagaruwa musamman bayan daukewar jinin al’ada.
*Sa pant busasse
*Tsarki da ruwan dumi
Tafiya da pant
*Tafiya da takalmi
*Rage yawan dadewa akan masai
*Rage yawan cin albasa
* Rage yawan amfani da tafarnuwa
A Wani Bangare Kuma
Idan mace tayi ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta sabida shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini .
Yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan mar-mari
Wake
kifi
Nama
kwai da sauransu
Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su
Salat
kabeji
Alayyafo
zogole
Lemu
kankana
Apple dasauransu .
Wanda cin abinci lafiyayya yana karawa mata jini , lafiya , yana karawa yaron da yake cikib ta lafiya da kaifin basira .
Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane
mace mai juna biyu baikamata tadinga aikin wahala sosai ba , yakamata tadinga hutu ko wacce rana .
idan mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibity domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ,ko zai yakawo matsaka ga yaron cikinta .
tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .
maccen da take yawan amai yakamata tayi amfani da busheshshen abinchi wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .
Zuwa awu (Antenatal) yana da amfani sosai wanda alokocin awu za a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki .
Kuma ana auna aga wassu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su da wuri.