Mutane da dama suna neman magani da kuma hanyar da zasu bi domin tabbatar da ganin komai yayi kyau, amma kuma abin yana gagara sakamakon/sanadin rashin yin magana ko kuma taɓo batun ɓangaren ga makusanta, ƴan uwa, abokai da kula masana a fannin lafiya.
Don haka duk wanda yake da matsalar ƙarancin sha’awa, to yayi sauri da hanzari wajen neman magani domin gyaran ɓarakar da zata iya faruwa a gaba tsakanin sa da mai ɗakinsa.
Saboda idan ta bangaren namiji ne matsalar to tabbas macen zata nemi wanda zai iya biya mata bukatar ta ta kowacce hanya, babu ruwanta da abinda da sakamakon dai haifar matukar za’a gamsar da ita.
Haka idan matsalar da bangaren mace ne, namiji zai iya yin dukkan abinda yaga dama domin jindadi da kuma walwalar sa a wajen gida, ko kuma ya karo wata matar da zata iya maye wurinki a don gamsar da shi.
Idan ana son a magance, a nemi kayan haɗi kamar haka :
Man Yansun
Garin Habba
Garin Yansun
Yadda Zaki Haɗa :
Za’a samu garin habba da garin yansun sai a hadesu guri daya a tafasaa, idan ya tafasa sai kuma a tace ruwan a zuba man yansun din a cikin ruwan. Daga nan kuma sai ana juya shi da cokali ko wani tsinke mai kyau yadda dai kame jikin sa.
Haka za’a na shan wannan hadi har tsawon sati biyu.
Allah yasa mudace.