Wani 'dan Najeriya mai suna Wale Oladapo ya koma da zama Canada a 2016 kuma ya bude gidan biredi bugun kato a kasar Biredin ya kasance mai taushi wanda jama'a da dama suke yabawa kuma ya yadu har zuwa yankunan kasar Yace akwai rassan gidan biredin a Waterloo, Windsor, Ottawa da Calgary yayin da wasu suka karba sunan suna yin irin shi 

Kwastomomi a Canada sun yabawa wani gidan biredi na 'dan Najeriya mai suna Grey Matlock Bakery da ke Brampton, Ontario kan yadda yake yin biredi bugun kato mai laushi. 

Shi dai irin wannan biredin a arewacin Najeriya ana kiransa da Bugun kato yayin da kudanci ake kiransa da biredin Agege, wani yankin jihar Legas. Biredi mai matukar taushi.

'Dan Najeriya mai suna Wale Oladapo ya bude gidan biredin a Brampton bayan komawa Canada da yayi a 2016.


Previous Post Next Post