Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan canza takardun kudi da bankin CBN ya yi Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya da mugun nufi a kan APC Gwamnan Jihar Kano yana ganin Godwin Emefiele ya kawo tsarin ne saboda ya rasa samun takara 

Abuja - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya zargi Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da canza kudi saboda ya gagara samun tikiti. Da ya zanta da BBC Hausa bayan Gwamnoni sun hadu da shugaban kasa, Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Gwamnan CBN da mugun nufi. 

A ranar Juma’a, Gwamnan na Kano ya ce Mista Godwin Emefiele bai so a shirya zabe a Najeriya, ya kuma ce sun koka da wahalar da canjin kudin ya jawo. 

Gwamnan yake cewa tsarin da babban bankin CBN ya fito da shi na canza manyan takardun kudi ya yi hannun riga da ra’ayin jam’iyyar APC da ke mulki. 
Haushin rasa takara ne? Dr. Ganduje yana zargin bita-da-kulli ne Gwamnan bankin yake yi saboda Bola Tinubu ya doke shi a zaben tsaida gwanin ‘dan takaran shugaban kasa. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Zargin da irinsu Ganduje suke yi wa Emefiele shi ne yana kokarin damkawa 'yan adawa nasara. Zargin da har yanzu shi Gwamnan bankin bai tanka ba. 


Previous Post Next Post