CBN ya bayyana cewa wasu 'yan Najeriya masu halin aje kuɗi a gida ne suka jawo karancin takardun naira Rashidat Monguno, Darakta a CBN ta ce mafita ɗaya ce masu jibge kuɗi a gidaje su fito da su a ci gaba da hada-hada A cewarta, CBN ya fitar da isassun kuɗade amma har yanzun ana fama da karancinsu saboda halayen wasu tsiraru.

 Babban bankin Najeriya (CBN) ya alaƙanta musabbabin ƙarancin sabbin takardun naira da halin wasu 'yan Najeriya na jibge kuɗin a gidajensu. Daraktan sashin baiwa kwastomomi kariya a CBN, Rashidat Monguno, ita ce ta faɗi haka a Kwara ranar Alhamis yayin da ta je duba yadda bankunan Microfinance ke biyayya ga tsarin.


Previous Post Next Post