Akwai kamshin gaskiya a rade-radin da ake yi game da kulla-kullan da wasu ke yi kan Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai wasu na kusa da fadar shugaban kasa da ke shiryawa Tinubu manakisa Don nuna goyon bayanta ga batun, matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta daura bidiyon El-Rufai a shafinta na soshiyal midiya 

Aisha ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, yan awanni bayan El-Rufai ya yi magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV. Matar shugaban kasar wacce ita ke jagorantar jirgin yakin neman zaben Tinubu ta yi wa wallafar tata take da: 

Gwamnan na jihar Kaduna dai ya ce wadannan mutane da bai bayyana sunansu ba suna fakewa a bayan Shugaba Buhari suna kokarin cimma kudirinsu na ganin Tinubu ya fadi zabe. 

Da yake martani, ministan labarai, Lai Muhammad ya sake nanata matsayin shugaban kasa na mayar da hankali 

Ja kuma bayyana cewa su dai basu da masaniya kan wadanda ke yi wa dan takarar na APC zagon kasa a cikin fadar gwamnatin. A wani labarin, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin Najeriya a 2023 abun dariya ne domin dai aikin shugabancin kasa ba na yan shekaru 40 zuwa 50 bane.. 
Previous Post Next Post