Matashi Salisu bai taba sanin sasanci da tsaida kwantar da tarzoma da shiga tsakanin makwabtansa 2 a Kano zaiyi sanadiyyar nakasarsa ba ta hanyar da bai yi tsammani ba. Lamarin wanda ya auku a yankin Fagge cikin garin Kano yayi sanadiyyar da Husaini, matashin mai shekaru ashirin da daya yayi rashin hannunsa sakamakon soka masa wuka da wani hatsabibi, Abubakar Ayuba, da ake kira da Namama a yankin yayi.
√City & crime: sun tattaro yadda rikici ya barke tsakanin Namama da matashi Abdullahi Muhammad, wanda ake kira da Alhaji Ozil, a karshen watan Maris, wanda yayi tsanani yayin da Salisu ya ga ya dace ya shiga lamarin don kwantar da rikicin amma daga karshe aka soka masa wuka wanda yayi sanadiyyar shigar cutar tatanos. Yayin labarta yadda lamarin ya auku a gadon asibitinsa inda aka cire masa hannun, Hussaini yayi kira da babbar murya ga hukumomi da su samar masa 'yancinsa saboda bai taba tunanin rasa hannunsa ba.