Manchester United doke takwararta Manchester City da ci 2-1 a wasan hammayya da ƙungiyoyin biyu suka buya a filin wasa na Old Trafford.

City ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Jack Grealish a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na rage yawan tazarar maki da ke tsakaninta da Arsenal wadda ke ta ɗaya a kan teburin Premier.

To sai dai haƙar City ba ta cimma ruwa ba, bayan da Bruno Fernandes ya farke ƙwallon ana saura minti 12 a tashi wasan, duk da kasancewar Marcus Rashford a cikin da'irar satar gida.

Minti huɗu bayan hakan ne kuma Marcus Rashford ɗin ya ƙara ta biyu bayan da ya zura ƙwallon da Alejandro Garnacho ya bugo masa.

Da wannan sakamako United ta koma ta uku a kan taburin maki ɗaya tsakaninta da City wadda ke matsayi na biyu, maki biyar tsakaninta da Arsenal ta ɗaya.

Previous Post Next Post