Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta yi gargaɗin cewar babban zaɓen ƙasar da ke tafe ka iya gamuwa babban ƙalubalen sokewa a wasu mazaɓun ƙasar idan matsalar tsaro ta ci gaba da addabar wasu sassan ƙasar.
Shugaban cibiyar bayar da horo ta hukumar zaɓen Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ne ya bayyana gargaɗin ranar Litinin a lokacin duba kayan aikin horaswa na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce ''duka mun sani cewa tsaro a lokacin zaɓe abu ne mai muhimmanci ga dimokradiyya , domin tabbatar da samun sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasa''.
“Dan haka a cikin shirye-shiryen da hukumarmu ke yi game da zaɓen 2023, dole mu yi iya bakin ƙoƙarinmu domin tabbatar da cikakken tsaro ga ma'aikatanmu da kayan aikin zaɓe da kuma hanyoyin da za mu bi wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara'', in ji Farfesa Zuru.
“Amma idan ba a magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta ba, hakan zai haifar da soke zaɓen ko kuma ɗage shi a mazaɓu da dama, lamarin da kuma zai shafi bayyana cikakken sakamakon zaɓen, abin da kuma ka iya haifar da wasu matsaloli da suka shafi kundin tsarin mulki''.
Hukumar zaɓen ƙasar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar.